Kasar Turkiya zata maida ‘yan ci-rani 12,474 zuwa kasashensu

Kasar Turkiya zata maida ‘yan ci-rani 12,474 zuwa kasashensu

-Kasar Turkiya za ta maida 'yan cin-rani 12,474 daga Istanbul zuwa kasashensu

-Ofishin gwamnan Istanbul ne ya fitar da wata sanarwa ta musamman inda aka bayyana adadin 'yan gudun hijirar Syria dake garin

-Bincike ya nuna akwai mutune sama da miliyan guda wadanda suka shigo kasar tare da rajista a matsayin 'yan gudun hijira

Gwamnatin kasar Turkiya a ranar Alhamis 1 ga watan Agusta, 2019 ta bada sanarwar korar ‘yan ci-rani 12,474 wadanda aka kama a babban birnin kasar na Istanbul.

An samu kama ‘yan ci-ranin ne wadanda suka shigo kasar ta harmatacciyar hanya a tsakanin 12 ga watan Yuli zuwa yau din nan.

KU KARANTA:Yadda Gwamnatin tarayya ta kubutar da N500bn daga barayi – Babban jami’in Gwamnati

A wani zancen da ya fito daga ofishin gwamnan Istanbul, ya bayyana mana cewa jami’an tsaro sun samu nasarar damke mutum 2,630 wadanda suka yo gudun hijira da kasar Syria.

Ministan harkokin cikin gidan Turkiya, Suleiman Soylu ya bada wata sanarwa a makon da ya gabata inda yake cewa, “ ‘Yan gudun hijirar Syria zamu aika da su sansanin ‘yan gudun hijiran da muke da shi a maimakon mu mayar da su zuwa kasar su, saboda sun shigo nan ne domin neman tsira.”

A farkon watan Yuli, ofishin gwamnan Istanbul ya bada umarni ga ‘yan gudun hijiran da ba su da rajistar zama a Istanbul da su koma zuwa garin da aka yi masu rajista kafin ranar 20 ga watan Agusta.

Haka zalika, hukumar kula da shige da ficen kasar Turkiya ta bayyana mana cewa akwai jimillar ‘yan gudun hijira miliyan 1.06 wadanda aka yiwa rajista a birnin Istanbul, inda kuma mutum 547,000 daga cikinsu ‘yan asalin kasar Syria ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel