An gurfanar da matashi da laifin cizon mace a ƙirji

An gurfanar da matashi da laifin cizon mace a ƙirji

Matsananciyar wahala yayin bai wa hammata iska, ta sanya wani matashi mai shekaru 22, Precious Michael, ya kai hakwara kan ƙirjin wata Mata. Laifin da ya sanya aka gurfanar da shi a gaban kotun majistire ta birnin Asaba a jihar Delta.

Hukumar 'yan sandan jihar sun zargi wannan matashi da laifin cin zarafi da ya sabawa sashe na 355 da kuma na 451 cikin dokokin miyagun laifi da gwamnatin Delta ta shimfida tun a shekarar 2006.

Matar da wannan lamari ya auku a kanta, ta kuma yi karar wanda ake zargi da laifin kece mata riga wadda darajarta ta kai kimanin naira dubu hudu.

Alakaliyar kotun ta majistire Edith Anumodu, ya bayar da belin Precious a kan kudi naira dubu hamsin bayan da jami'an 'yan sanda suka tsare shi a katararsu.

Ta kuma dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Agusta kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito.

KARANTA KUMA: Buhari yayi murnar yiwa Kemi Badenoch nadin minista a Birtaniya

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, matsananciyar wahala ce ta sanya Precious ya yi cizon abokiyar fadansa a ƙirji bayan ya sha maƙara yayin da ta sanya shi a maƙata. Ya kuma samu nasarar tumbuke mata hakori guda.

A wani rahoton mai nasaba da wannan, wani magidanci mai shekaru 40 a duniya, Simon Eneche, ya shiga hannun hukuma a watan Janairun 2018 bayan wata sa'ainsa ta sanya ya lakadawa wata mata dukan tsiya a jihar Delta.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel