Yanzu-yanzu: Buhari ya rattaba hannu kan sabbin dokoki biyu

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattaba hannu kan sabbin dokoki biyu

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan sabbin dokokin biyu da majalisar dokokin tarayya suka kaddamar masa.

Babban hadimin shugaban kasa kan harkokin majalisar dattawa, Ita Enang, ya bayyana hakan ne wani hira da manema labarai a ranar Laraba, birnin tarayya Abuja.

Wadannan dokoki sune dokar canza kwalejin ilimin jihar Kebbi da dokar kungiyar masu zanen gida a Najeriya.

Ya ce game da dokar kwalegin ilimin noman tarayya dake dake garin Zuru, jihar Kebbi an mayar da ita jami'ar aikin noman tarayya.

Dame da dokar kungiyar masu zanen gida kuwa, an kara kudin taran da ake cin masu zane daga N1000 zuwa N500,000.

KU KARANTA: Jerin mutane 20 dake rike da bashi gwamnati N5trn

Yayinda aka tambayeshi kan wasu dokokin da Buhari ya ki sanya hannu,ya ce hakan ya faru ne bisa ga wasu dalilai masu muhimmanci.

Kana yan jarida sun tanbayeshi lokacin da Buhari zai rantsar da ministocin da majalisa ta tabbatar, yace: " Idan shugaban kasa ya karbi takardar tabbatarwa daga majalsar dokoki, zai zabi rana domin sanarwa wadanda ya zaba."

A ranar Talata, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya nada kwamiti na musamman domin kwato basussukan gwamnati dake hannun wasu yan Najeriya 20 na kimanin tirilyan biyar.

Hukumomin da aka baiwa aikin kwato basussukan sune hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, hukumar NFIU, hukumar ICPC, sakataran ma'aikatar Shari'a da ma'aikatar sakataren Sufuri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel