Yunwa ta kashe kananan yara 12 a jahar Gombe, an kwantar da 1,732

Yunwa ta kashe kananan yara 12 a jahar Gombe, an kwantar da 1,732

An samu mutuwar kananan yara guda 11, tare da wasu guda 1, 732 da yanzu haka suke kwance a asibitoci daban daban a duk fadin jahar Gombe sakamakon rashin isashshen abinci mai gina jiki, inji rahoton jaridar Blue Print.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’in kula da abinci ma gina jiki na jahar Gombe, Usman Baraya ne ya bayyana haka a ranar Talata, 30 ga watan Yuli yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace an samu sauki a kan shekarar 2018 inda yara 99 suka mutu, aka kwantar da 13,594.

KU KARANTA: Fadi ba’a tambayeka ba: Jam’iyyar APC ta yi kira ga Atiku ya sanya ma bakinsa linzami

Usman yace daga cikin yara 15,326 da aka kwantar a asibitoci daga shekarar 2018 zuwa 2019, an sallami yara 12, 880 bayan sun samu cikakken lafiya, ya cigaba da cewa asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya,UNICEF sun taimaka matuka ta hanyar tallafin abinci da suke bayarwa.

Sai dai Baraya ya bayyana damuwarsa da cewa a duk lokacin da UNICEF suka janye wannan tallafi nasu za’a sake samun barkewar cututtukan da suka danganci rashin abinci mai gina jiki a jahar Gombe, idan har ba’a dauki matakin daya kamata ba.

Majiyarmu ta ruwaito an gano wani cibiyar karbar abinci mai gina jiki na kananan yara dake kauye Gidan Magani inda aka kwashi watanni hudu ba’a kai musu irin wannan abinci ba, wanda hakan ya ta’azzara cututtukan rashin abinci mai gina jiki a yankin.

Shima Baraya ya bayyana cewa a karamar hukumar Gombe ba’a sake samun abincin ba tun daga 25 ga watan Janairun 2019, har sai ranar 19 ga watan Yuli, don haka yake ganin ba lallai a sake samun abinci ba sakamakon gwamnatin jahar ta gaza wajen bayar da nata kudin da UNICEF ke bukata wajen sayo abincin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel