Mace kawai zan iya aura sabo da ni Sarauniya ce - Basarakiyar Najeriya

Mace kawai zan iya aura sabo da ni Sarauniya ce - Basarakiyar Najeriya

Omu Anioma, Martha Dunkwu, ita ce basarakiyar kasar Anioma, wacce ta mamaye kananan hukumomi 9 a jihar Delta. Mutanen yankin Anioma 'yan kabilar Igbo ne da ke Delta, wadanda tekun 'River Niger' ya raba da 'yan kabilar Igbo da ke yankin kudu maso gabas.

Yayin wata hira da gimbiya Martha, ta bayyana cewa a matsayinta na sarauniya, mace kawai za ta iya aura.

Da aka tambaye ta "a matsayinki na sarauniya, ya kike ji a rayuwarki, kasancewar ba ki da miji balle 'ya'ya?

Sai ta ce, "da zarar an bawa macen da ke da aure sarautar Omu, dole ta bar gidan mijinta ta koma gidan mahaifinta. Daga lokacin ta zama namiji. Za a gina mata fada a gidan mahaifinta kuma za ta daina mu'amala da mijinta duk da zai iya zuwa fada domin ya gaishe ta, a hakan ma ba zai dade a fadar ba.

"Mijinki ba zai zo ya kwanta da ke ba, kuma ba zaki kara yi masa wata dawainiya ta ma'aurata ba. Yaran da kuka haifa kafin a nada mace a sarautar Omu, zasu cigaba da zama mallamkin ki ne.

DUBA WANNAN: Manyan daliliai uku da suka tilasta Buhari ya fasa bawa Ambode minista

"Idan mace ba ta haihu ba ko ta haifi iya yaro ko yarinya daya a lokacin da aka nada ta kuma ta na sha'awar samun karin haihuwa, sai dai ta auri mace, wacce za ta haifa mata wasu yaran saboda ba zata kara rayuwa da namiji ba.

"Yaran da kika haifa da yaran da matar ki ta haifa miki duk zasu zama mallakar ki ne, kuma suna da hakki iri daya a kan ki, babu wani banbanci a tsakaninsu. Ni yanzu ina da yaro daya duk da aka haifa min duk da ban taba aure ba.

"A ra'ayina aure magana ce ta zabi amma da alfahari. Ina da yaro guda daya wanda yanzu lakcara ne a jami'a. Ni namiji ce kuma mace duk a lokaci daya. Ba na karkashin wani namiji, ni wata halitta ce ta daban. An bani duk hakki da ikon da namiji ke da shi lokacin da aka nada ni."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel