Kuma dai, uwargida ta cakawa mijinta wuka sau biyu a ciki a jihar Kaduna

Kuma dai, uwargida ta cakawa mijinta wuka sau biyu a ciki a jihar Kaduna

A ranar Juma'a, wata mata mai suna Aisha ta cakawa mijinta, Yahaya Mayaki, wuka sau biyu a ciki sakamakon wani sabani da suka samu na auratayya a gudansu dake unguwar Sardauna Crescent, mun samu rahoto.

Mun tattaro cewa ma'auratan sun samu sabani a daren jihar kafin faruwar wannan abu.

A cewar dan'uwan mijin mai suna, Ahmed Maiyaki, yace:

"Da safiyar yau, yayana DanAsabe ya tsallake rijiya da baya yayinda matarsa, Aisha, tayi kokarin hallakashi. Yana asibiti yanzu."

"Aisha ta nufi watsawa mijin tafasasshen ruwan zafi yayinda ya tashi domin Sallar Asuba, ta watsa masa ruwa amma ya samu sa'an kaucewa, sannan ta jefa masa tukunyar ruwan zafin.

"Yayinda ya sake kaucewa jifan, sai ta dauki wuka ta caka masa a cikinsa sau biyu."

"Abin ban mamakin shine shekarun biyar suna tare kuma sun haifi yaro daya, ba'a taba zaton tanada hali da zai iya tuntsurata aikita irin wannan abu ba."

Yayinda aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda, DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da faruwa kuma an tsare matar.

Muhimmaiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel