Ajali ya yi kira: Ruwa ya cinye wani matashi dan shekara 23 a jahar Kano

Ajali ya yi kira: Ruwa ya cinye wani matashi dan shekara 23 a jahar Kano

Wani matashi dan shekara 23, Aminu Abdullahi ya gamu da ajalinsa yayin da yake wanka a cikin wani korama dake unguwar Hotoro cikin karamar hukumar Nassarawa ta jahar Kano, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin hukumar kwana kwana ta jahar Kano, Saidu Muhammad ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 26 ga watan Yuli, inda yace lamarin ya auku ne da safiyar Juma’a a lokacin da matashin ya tafi tafkin don yin wanka.

KU KARANTA: Ministan Buhari ya bayyana babban dalilin da yasa gwamnati ta ki sakin Dasuki da Zakzaky

“A yau wani mutum mai suna Habila John ya kiramu da misalin karfe 8:30 na safe yana shaida mana cewa ya hangi wata gawa tana yawo a saman ruwan koramar, samun wannan labari muka garzaya da gaggawa zuwa inda lamarin ya auku.

“Mun isa wurin a daidai 8:35, isarmu keda wuya muka ciro Aminu, amma ko a lokacin ya fita hayyacinsa, inda muka mikashi ga jami’an Yansanda, amma har yanzu bamu gano musabbabin mutuwarsa ba.” Inji shi.

Daga karshe Saidu ya shawarci jama’a musamman iyaye da dakatai dasu tsawata ma yaransa daga shiga cikin ruwa suna wanka, domin hakan zai iya zuwa da hatsari, wanda sai dai Allah Ya kiyaye kawai.

A wani labarin kuma, Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Jigawa ta kama wani matashi dan shekara 25 mai suna Jamilu Harisu sakamakon kashe mahaifinsa dan shekara 70 da yayi.

Jamilu ya kashe mahaifin nasa ne a halin maye bayan ya sha miyagun kwayoyi ya koshi, inda ya bi sawun mahaifin nasa zuwa gona, ya tarar dashi yana aiki, a can ne ya halaka shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel