Wani mahaukaci ya kashe karamin yaro, ya jikkata mutane 3 da fartanya a jIgawa

Wani mahaukaci ya kashe karamin yaro, ya jikkata mutane 3 da fartanya a jIgawa

Wani mutumi mai tabin hankali, Abdulkarim Mato ya halaka wani karamin yaro mai shekara 2 sakamamon fartanya da yayi a lokacin da haukarsa ya tashi, a kauyen Dujah dake cikin karamar hukumar Miga ta jahar Jigawa.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito karamin yaron dan shekara biyu mai suna Idris Ibrahim nan take yam utu ko shurawa bai yi ba, sa’annan Mato ya cigaba da farautar duk wanda ya yi ido hudu dashi.

KU KARANTA: Ministan Buhari ya bayyana babban dalilin da yasa gwamnati ta ki sakin Dasuki da Zakzaky

Majiyar Legit.ng ta ruwaito haukan na Mato ya motsa ne a daidai lokacin da mazan garin suka tafi gona, inda baya da karamin yaron daya kashe, Mato ya kai ma wasu mata guda uku hari, a sanadiyyar haka ya ji musu rauni.

Sai dai an yi sa’a aka garzaya dasu zuwa Asibitin kwararru dake garin Jahun cikin karamar hukumar Jahun domin samun kulawar gaggawa, kamar yadda kaakakin Yansandan jahar Jigawa, SP Audu Jinjiri ya tabbatar.

“Haukan mutumin ya tashi ne bayan yan mazan garin sun tafi gona, inda ya kai ma Idris Ibrahim hari yar ya kasheshi, sa’annan ya bi wasu mata a guje ya raunatasu, matan sun hada da Halima Mato yar shekara 50, Rashida Rabiu mai shekaru 23, da Mauluda Muhammed yar shekara 3.

“A yanzu dai an mikashi zuwa asibitin mahaukata dake garin Kazaure cikin karamar hukumar Kazaure domin duba lafiyar kwakwalwarsa.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Yansanda sun kama wani matashi daya kashe mahaifinsa da fartanya yayin da yake aiki a gonarsa dake kauyen Makku cikin karamar hukumar Garki, jahar Jigawa, sai dai rahotanni sun bayyana matashin yana cikin mayen kayan shaye shaye ne a lokacin daya tafka wannan ta’asa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel