An daure Lebura daya keta mutuncin karamar yarinya yar shekara 8

An daure Lebura daya keta mutuncin karamar yarinya yar shekara 8

Wata babbar kotun majistri dake zamanta a garin Kaduna ta bada umarnin garkame wani katon banza dake sana’ar leburanci, Abubakar Mohammed a gidan Kurkuku sakamakon gurfanar dashi da aka yi a gabanta kan zarginsa da yi ma wata yarinya fyade.

Rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta bayyana cewa Alkalin kotun ta bayyana bacin ranta da jawabin da aka yi mata game da tuhumar da ake yi ma Leburan, wanda ake zargi da keta mutuncin karamar yarinya yar shekara 8.

KU KARANTA: Arzikin kasa: An kasafta naira biliyan 762 tsakanin jahohi, kananan hukumomi da gwamnatin tarayya

Da farko dai majiyar Legit.ng ta ruwaito dansanda mai shigar da kara, Inspekta Sunday Baba ya bayyana ma kotu cewa leburan ya aikata wannan laifi ne a ranar 11 ga watan Yuni a unguwar Sabon Gari, dake garin Zariya.

Dansandan ya bayyana cewa leburan ya yi ma yarinyar wayau ne inda ya jata cikin wani sundukin kwantena, a ciki ya yi mata fyade, wanda ya bayyana laifin cewa ya saba ma sashi na 207 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Kaduna.

Sai dai Leburan ya tsaya kai da fata atafau bai aikata laifin da ake tuhumarsa dashi ba, har ma ya nemi kotu ta bada belinsa, sai dai Alkalin kotun, mai sharia Hajara Dauda ta ki amincewa da bukatarsa, inda ta koka kan yawaitan laifukan fyade a jahar kaduna.

Alkali Hajara ta umarci Yansanda su mika wannan magana zuwa ofishin babban jami’I mai shigar da kara na jahar Kaduna don samun shawarar abinda ya kamata, sa’annan ta umarci a garkame mata Leburan a gidan yari.

Daga karshe mai sharia Hajara Dauda ta dage zaman sauraron karar zuwa 14 ga watan Agustan shekarar 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel