‘Yan Sanda sun damke wanda ta kwararawa boyi-boyin borkono a al’aura

‘Yan Sanda sun damke wanda ta kwararawa boyi-boyin borkono a al’aura

Mun samu labari cewa jami’an ‘yan sandan Najeriya da ke jihar Anambra sun kama wata Mata mai suna Charity Effiong da zargin zuba barkono a mafitsar yarinyar da ke yi mata aiki a gida.

Wannan Mata ta barbada mata barkonon ne a dalilin zargin ta da ta ke yi na sace mata kudi N260, 00. Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, shekarun wannan Yarinya duka-duka 12 a Duniya.

Rahotannin sun kuma nuna cewa wannan abu ya faru ne a layin Nzekwe da ke cikin babban birnin jihar Anambra watau Awka. Wannan yarinyar ta na aji hudu ne na makarantar firamare.

Yarinyar da a ka barbadawa barkonon ta fito ne daga jihar Ebonyi. Mai gidar ta yi wa wannan yarinya zindir ne inda ta rika zuba mata barkono mai yaji a cikin al’aurarta domin azabtar da ita.

Bayan ganawa wannan yarinya azaba ne Uwargijiyarta ta, ta fatattake daga cikin gida da kimanin karfe 10:30 na dare. Daga baya ne wasu mutane su ka tsince ta a kan titi ta na ta faman rusa kuka.

KU KARANTA: An nada kwamiti da zai binciki zargin fyaden da a ke yi wa ‘Yan mata a Makarantu

‘Yan jarida sun ce wannan yarinya da a ka gallazawa azaba ta bada labarin abin da ya auku inda ta nuna yadda Mai gidar ta, ta saba yi mata ‘dan karen duka da zarar an sa ta wani aiki a gida.

Wanda ta tsinci yarinyar kuwa, ta bayyana cewa sai da ta shafe fiye da mintuna 30 kafin radadin borkonon ya fita. Masu kare hakkin yara a jihar Anambra sun yi Allah-wadai da wannan zalunci.

Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an yi ram da Madam Effiong inda a ka shigar karar ta a gaban kotu. Matar ta yi kokarin nunawa ‘yan sanda cewa wasu ne su ka sace mai yi mata aikin gidan.

Kakakin ‘yan sanda na Anambra, Haruna Mohammed, ya ce an maida wannan yarinya gaban Iyayenta. Matar kuma ta ce ta tube yarinyar ne domin laluba inda ta boye kudin da ta sace mata

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel