Majalisar wakilai ta sake dawo da kudirin neman kafa 'Peace Corps'

Majalisar wakilai ta sake dawo da kudirin neman kafa 'Peace Corps'

A ranar Laraba ne mambobin majalisar wakilai suka amince da sake dawo da kudirin neman kafa hukumar tsaro ta 'Peace Corps' domin kara yi wa tanade-tanaden kunshin kudirin duba na tsanaki kafin amincewa da shi.

Majalisar ta ce za ta amince da dokar bayan kwamitin ta da ta dora wa nauyin alhakin sake duba kudirin ya kammala aikinsa na yin kwaskwarima da gyaran fuska ga kunshin tsare-tsaren neman kafa hukumar.

Kudirin neman kafa 'Peace Corps' ya tsallake karatu na farko a majalisar ta 9 a ranar 3 ga watan Yuli, 2019.

Honarabul Mohammed Tahir Monguno, bulaliyar majalisar wakilai, ne ya sake tanade kudirin tare da sake gabatar da shi a zauren majalisar.

Da ya ke sake gabatar da kudirin a zauren majalisar ranar Talata, Monguna ya ce doka da tsarin majalisa ya yarda mamba a majalisa ya sake dawo da kudiri domin tattauna wa a kansa bayan ya yi masa kwaskwarima.

Ko a zangon mulkin shugaba Buhari na farko sai da majalisun kasa (majalisar wakilai da dattijai) suka amince da kudirin kafa hukumar 'Peace Corps' amma shugaban kasa ya ki rattaba masa hannu domin ya zama doko.

Dakta Dickson Akoh, kwamandan 'Peace Corps' na kasa, ya bayyana jin dadinsa tare da mika godiya ga majalisar da shugabancinta bisa sake waiwayar kudirin neman kafa hukumar da ya kirkira.

A hirarsa da majiyar Legit.ng ta wayar tarho, Akoh ya bukaci dukkan mambobin kungiyar 'Peace Corps' su kara hakuri tare da dage wa da addu'o'i domin kudirin ya samu tsallake wa a wannan karon.

A cewarsa, yanzu an gyara dukkan wasu bangarori na kudirin da suka jawo shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ki amincewa da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel