Yanzu-yanzu: Komai ya kankama domin tantance ministocin Buhari

Yanzu-yanzu: Komai ya kankama domin tantance ministocin Buhari

- An fara tantance ministocin da shugaba Buhari ya aika majalisa

- Uchecukwu Ogar na jihar Abia ne kan magana yanzu

Komai ya kankama domin fara tantance ministocin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar majalisar dattawa.

Shugaban masu rinjaye, Abdullahi Yahaya, ya gabatar da sunayen ministocin kuma majalisar ta amince a fara tantancesu.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa za'a fara yanzu zuwa karfe 1 na rana domin hutun rabin lokaci da Sallah, sannan a dawo karfe 2.

Daga cikin wadanda za'a tantance a yau sune tsohon ministan Ilimi, Adamu Adamu; tsoon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; Sunday Dare; tsoho gwamnan Benue, George Akume; Mustapha Shehuri, Ogbonnaya Onu da Adeleke Mamora.

KU KARANTA: Buhari ya yabawa Salihin Sojan da ya dawo da N15m da ya tsinta

A jiya, shugaba Muhammadu Buhari ya aika sunayen mutane 43 da yake niyyar nadawa a majalisar zantarwarsa.

Daga ciki akwai tsaffin gwamnoni, tsaffin ministoci 14, sauran kuma sabbin mininstoci. Daga cikin sabbin akwai babban malamin addini, Sheikh Isa Ali Fantami; kakakin shugaba Muhammadu a zaben 2019, Festus Keyamo, da shugabar hukumar fansho, Sharon Ikeazor.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel