An tono tsuliyar dodo: An kashe Soji 2 a Bayelsa, Sojoji sun tayar da kauyen

An tono tsuliyar dodo: An kashe Soji 2 a Bayelsa, Sojoji sun tayar da kauyen

Rundunar sojin Najeriya a ranar Talata sun kai farmaki kauyen Azagbene dake karamar hukumar Ekeremor a jihar Bayelsa inda suke neman yan bindigan da suka kashe jami'an Soji biyu.

An samu labarin cewa wasu yan tayar da zaune tsaye sun hallaka jami'an soji biyu masu gadin kamfanin man feturin Shell SPDC.

Bayan binciken da aka gudanar, sojojin sun gano cewa yan bindigan sun gudu cikin kauyen shi yasa suka dira kauyen da sassafe suna kona gidajen kauyen.

Majiyoyi sun bayyana cewa wannan ya tilasta mazauna garin guduwa cikin daji domin ceton rayuwarsu.

KU KARANTA: Bayani game da sabbin ministoci daga jahar Kaduna

Kungiyar matasan Ijaw IYC sun nuna bacin ransu kan kisan Sojojin amma suna kira ga hukumar soji su bi a hankali kada su tsanantawa rayukan sauran al'ummar kauyen.

Shugaban kungiyar, Kennedy Olorogun, a jawabin da ya saki ya yi kira da hukumar ta hada kai da kungiyar IYC wajen gano wadanda suka aikata wannan aika-aika.

A wani labarin kuma, Jami'an yan sandan jihar Jigawa sun damke wani matashi dan shekara 25, Jamilu Harisu, da laifin kashe mahaifinsa mai shekaru 70.

Matashin, wanda ake zargi ya aikata aika-aikan ne saboda ya debi kwayoyi kafin ya kai wa mahaifinsa hari a gona.

Harisu ya kashe mahaifinsa ne a kauyen Makku dake karamar hukumar Garki na jihar Jigawa, inda ya buga masa fatanya a kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel