Babbar magana: Ina da tabbacin matata na kwanciya da wasu mazan a titi, amma na kasa yi mata magana - Wani mutumi ya koka

Babbar magana: Ina da tabbacin matata na kwanciya da wasu mazan a titi, amma na kasa yi mata magana - Wani mutumi ya koka

- An wallafa labarin da wani mutumi da yaje neman shawara wajen shararren masanin nan a bangaren zamantakewa da soyayya

- Mutumin ya bayyana cewa ya jima yana sanya ido akan matarsa, kullum za ta fita lafiya lau tare da kayanta tsaf-tsaf, amma kuma ba ta dawowa da dan kamfenta

- Ya bayyana cewa ya jima da fuskantar hakan, kuma shi baya so yayi mata magana wacce za ta saka su samu matsala a tsakaninsu, amma kuma zuciyarshi ta kasa daina raya mishi cewar tana cin amanarshi

Joro Olumofin, kwararre a bangaren zamantakewar aure da soyayya, ya wallafa labarin wani mutumi da ya tuntube shi akan zargin da yake yiwa matarsa na cewa sama da sati biyu tana dawowa gida ba tare da dan kamfenta ba, inda shi kuma yana da tabbacin cewa tana fita dashi.

A cewar labarin da ya wallafa a shafinsa na Instagram, mutumin yana aikin kirkire-kirkire na shafukan yanar gizo ne, inda yake aikinshi daga gida ba tare da ya fita ofis ba. Ya bayyana cewa sanya ido akan matar tasa na tsawon wasu lokuta shi kuma baya so fada ya shiga tsakaninsu.

KU KARANTA: Tonon silili: An kama wani ma'aikacin banki yana kokarin yin zina da wata budurwa a cikin banki

Ga abinda mutumin ya rubuta:

"Joro yanzu sama da sati biyu kenan matata tana dawowa gida ba tare da dan kamfenta ba. Za ta bar gida dashi a jikinta, amma kuma baza ta dawo tare da shi ba, na jima ina sanya ido a kanta, ban son rikici ya shiga tsakanina da ita shine yasa har yanzu ban yi mata magana ba.

"Da yawa daga cikin 'yan kamfenta dana sani sun bata, hakan na nufin tana cin amanata kenan. Na rasa yadda zanyi, na kasa cire tunanin tana zuwa ta kwanta da wani a zuciyata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel