An kama wani Uba da ya ke cin zarafin yayansa mata guda 3

An kama wani Uba da ya ke cin zarafin yayansa mata guda 3

Wata kotun babbar kotun majistri ta bada umarnin daure wani mutumi dan shekara 57 a gidan yari bayan ta samu kararsa da aka shigar gabanta bisa tuhumar da ake yi masa na cin zarafin yayansa mata guda 3.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dansanda mai shigar da kara, ASP Benson Emuerhi ya shaida ma kotu cewa mutumin mai suna Mojeeb Fashola ya aikata wannan danyen aiki ne a gidansa dake Ayetori, unguwar Ijanikin na jahar Legas a tsakanin watan Afrilu da watan Mayu.

KU KARANTA: Naira Biliyan 1 Sojoji su ka tsere da shi ba Miliyan 400 – Rahotanni

Dansanda ya shaida ma kotu cewa mahaifin yaran ya fara wannan kazamin aikin da da karamar diyarsa ne mai shekara 8, wanda yake soka hannunsa cikin farjinta, daga bisani sai ya fara bin manyan yayansa masu shekara 10 da 12, yana taba musu mama da mazaunansu.

Bugu da kari a lokacin da mahaifiyarsu ta gano abinda mijinta yake aikatawa da yaranta, sai ta yi barazanar kaishi kara ga Yansanda idan har bai bari ba, jin hakan tasa ya lakada mata dan banzan duka har da buga mata tabarya a kai .

Sai dai duk magiyar da Mojeeb ya yi a kotu, tare da musanta tuhume tuhumen da ake yi masa, hakan bai hanashi fuskantar fushin kotu ba, inda Alkalin kotun, Olufunke Sule-Amzat ta bada umarnina garkame matashi a kurkukun Kirikiri.

Sa’annan Alkalin ta umarci Yansanda su mika maganan zuwa ofishin babban jami’in gwamnatin jahar Legas mai shigar da kara don samun shawarar abinda ya kamata a yi, ta kuma dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel