Soyayya: Saurayi ya yi belin budurwarsa da aka kama saboda ta yi yunkurin cire masa mazakuta

Soyayya: Saurayi ya yi belin budurwarsa da aka kama saboda ta yi yunkurin cire masa mazakuta

Wani saurayi ya yi belin budurwarsa mai suna Blessing John wacce jami'an 'yan sanda suka kama saboda ta cije shi a mazakutarsa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa an kama tare da tsare Blessing ranar 5 ga watan Yuli a sashen binciken manyan laifuka (SCIID) na rundunar 'yan sandan Legas da ke unguwar Panti a yankin Yaba da ke jihar Legas, bayan ta ciji saurayinta a mazakuta domin kubutar da kanta daga yunkurin yi mata fyade, kamar yadda ta fada.

Wata majiyar 'yan sandan sashen SCIID ta shaida wa NAN cewa saurayin mai suna Johnson ya yi belin Blessing ne bayan an sallamo shi daga asibiti a ranar 15 ga watan Yuli. Ya kara da cewa sai da Johnson ya sayar da wasu kadarorinsa kafin ya iya biyan kudin magungunan da aka rubuta masa a asibiti.

Majiyar, wacce ba ta yarda a ambaci sunanta ba, ta bayyana cewa Johnson ya gaggauta zuwa ofishin SCIID domin yin belin Blessing bayan an sallamo shi daga asibiti.

"Ya zo tare da bayyana ma na irin son da ya ke yi wa budurwarsa, Blessing, kuma ya nemi a bashi belin ta tare da bayyana cewa bashi da bukatar a kai maganar gaban kotu.

DUBA WANNAN: Wata baiwar Allah ta rabu da mijinta saboda yafi son ta a kan mahaifiyarsa

"Sannan ya fada ma na cewa bai san lokacin da likitan asibiti ya sanar da 'yan sanda abinda ya faru ba, domin bai tuntube shi ba.

"Ya fada ma na cewa har yanzu ya na son budurwarsa kuma ya saka hannu a kan takardar yarjejeniyar karbar ta a kan beli," kamar yadda majiyar 'yan sanda ya shaida wa NAN.

An kama Blessing ne bisa zarginta da cizon Johnson a mazakuta, a yayin da ta ke kokarin ceton kan ta daga kokarin yi mata fyade.

Bayan an kama ta, Blessing ta shaida wa NAN cewa ta yi cizon ne yayin da ta ke cikin halin wuya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel