Sai na azabtar da mutane kafin na ke kashe su - Shugaban kungiyar asiri dan shekara 20

Sai na azabtar da mutane kafin na ke kashe su - Shugaban kungiyar asiri dan shekara 20

Rundunar 'Yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta sanar da cewa ta kama daya daga cikin shugabannin kungiyar asiri da ya dade yana adabar mutanen unguwannin Oworonsoki and Bariga a jihar.

'Yan sandan yaki da 'yan kungiyoyin asiri ne suka kama wanda ake zargin mai suna Diri Oyelesi dan shekara 20.

'Yan sandan sun ce Oyelesi ya amsa cewa tabbas yana kungiyar asiri tare da cewa yana da hannu cikin kisar wasu 'yan kungiyar asirin da ke adawa da shi a Oworonsoki.

DUBA WANNAN: Na yi wa 'yar ciki na fyade ne domin bata kariya - Mahaifi

'Yan sandan sun ce shugaban sashin yaki da 'yan kungiyar asiri, Uduak Edom ne ya jagoraci sauran jami'an zuwa kama Oyelesi bayan wani ya tsegunta musu inda ya ke buya.

Oyelesi ya amsa cewa wanda ya fara kashewa dan wani kungiyar asirin ne da ke da hannu wurin kisar dan uwansa.

'Yan sandan sun ce wanda ake zargin ya koka cewa tun shigarsa sa kungiyar asiri ta Eiye a 2014, bai amfana da wani ba ila aikata laifi, fyade, kisan kai, fashi da makami da shan miyagun kwayoyi a maimakon aikinsa na aski.

"Duk da cewa ba kungiya daya muka shiga da dan uwana ba, na dau alwashin sai na dauki fansa kan wadanda suka kashe shi. Haka ya sa na nemo sunayen wadanda ke da hannu cikin kisarsa a makonni shida.

"Daga nan kuma na shirya yadda zan kai musu hari. Na yi nazarin inda suka zuwa. Wata rana na kama daya daga cikinsu a wani layi kafin ya ankare na harbe shi.

"Ya fadi kasa ya yi kokarin tashi amma na danne shi. Na tambaye shi sunan sauran da ke da hannu cikin kisar dan uwa na. Da farko ya ki fada min amma daga baya ya fadi bayan na azabtar da shi. Kafin ya yi ihu neman taimako na kashe shi," inji wanda ake zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel