Wani magidanci ya yi ido biyu da damisa a kan gadonsa

Wani magidanci ya yi ido biyu da damisa a kan gadonsa

-Wani magidanci ya yi arba da damisa a kan gadonsa

-Wannan abin mamakin dai ya auku ne a jihar Assam dake kasar Indiya inda ambaliyar ruwa ta kashe dabbobi 92

-Ana zargin cewa damisar na daya daga cikin dabbobin gandun namun dajin Kaziranga wanda ambaliyar ta rufta da shi

An gano wata macen damisa da ta tsere daga wani gandun namun daji a jihar Assam wanda ambaliyar ruwa ta daidaita a kishingide kan gado a wani gida.

Ana zargin wannan damisar dai ta gudo ne daga gandun namun daji na Kaziranga inda dabbobi 92 suka mutu a ‘yan kwanakin nan sakamakon ambaliyar ruwa.

KU KARANTA:Kasashe 7 da yan Najeriya zasu iya ziyarta ba tare da biza ba

Bayan an gano damisar a cikin dakin, jami’an wata kungiya wadda ke fafutukar kare hakkin namun dawa ta isa gidan domin sama wa damisar hanyar fita zuwa daji.

Kamar yadda Gidauniyar Namun Dawa ta Indiya wato WTI ta ce, an fara ganin damisar ne ranar Alhamis kusa da wani babban titi.

Gidauniyar ta cigaba da cewa, babu shakka zirga-zirgar jama’ar wurin ce ta sanya damisar shiga cikin wannan gida dake daf da babban titin.

Rathin Barman wanda ya jagoranci cire damisar daga cikin gidan ya ce, ta shiga gidan ne da misalin 7:30 na safiyar Juma’a inda ta kwanta tayi baccin gaba daya ranar.

Rathin ya cigaba da cewa: “ Ta yi matukar gajiya kuma ta samu bacci mai kyau.” A bangaren maigidan kuwa, tattara iyalansa kaf ya yi lokacin da ya ga shigowar damisar.

“ Abin da ya bamu sha’awa shi ne babu wanda ya matsa mata ko kadan, domin ta samu hutu sosai. Muna matukar girmama namun dawa a wannan yankin namu.” Inji Barman.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel