Kasashe 7 da yan Najeriya zasu iya ziyarta ba tare da biza ba

Kasashe 7 da yan Najeriya zasu iya ziyarta ba tare da biza ba

Yan Najeriya na bukatar shiri sosai kafin su yi tafiya wata kasar. Samun Bizar fita daga Najeriya na da matukar wahala kasancewar fasfo din Najeriya ne na 83 a ‘yancin shiga kasashen duniya.

Duk da haka akwai kasashen da yan Najeriya marasa biza zasu iya zuwa muddin suna da fasfon Najeriya. Ga jerin sunayen kasashen kamar haka:

1-Rwanda

Mafi tsafta a Nahiyar Afirka, Kasar Rwanda ta zama masaukin baki da yan kasuwa. Bayan fama da kisan mummuke na yakin shekarar 1994 da kasar ta fuskanta, kasar ta sama canji sosan gaske. Yan Najeriya masu fasfo zasu iya samun biza yayin shiga Rwanda kan $100 kacal.

KU KARANTA:Hukumar DPR ta rufe gidajen mai 25 a Kano

2-Djibouti

Kasar tana daga cikin wurare mafi kyau a gabashin Afirka. Zaka iya samun biza yayin shiga kasar a farashi mai sauki, kasar tana da wurare masu kyau da za ka iya ziyarta kamar Kudiddifin Assal wato (Lake Assal).

3-Morocco

Sabbin ma’aurata zasu matukar jin dadin kasar Morocco saboda al’adu, yanayi da kyautatawan yan kasar ta Morocco. Kasar tanada wuraren bude ido, shakatawa, shaguna, na cin abinci da sauransu, wadanda ma’aurata bazasu gaji da wurin ba.

4-Cape Verde

Wani tsibiri ne a yankin Afirika ta yamma. Yanayin wurin nada gamsar da bako, masu hutu na ziyartar kasar saboda kyawunta.

5-Kenya

Kasar Kenya ta na da wurare masu kyawun gaske, tanada namun daji, da dumbin tarihi. Garuruwanta sun hada da Nairobi da Mombassa. Zaka iya samun biza yayin shiga kasar ta Kenya.

6-Uganda

Dimbin tarihin kasar Uganda ne ya sa yan Najeriya ke son ziyartar kasar sosai, suna da wurare kamar Lake Victoria da sauransu, ita ma za a iya samun biza yayin shiga

7-Sudan

Kasar Sudan na da wadatar sahara da namun daji tare da fadin kasa sosai. Matafiya daga Najeriya zasu iya samun biza yayin shiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel