Askarawan Hisbah sun kama mata masu zaman kansu guda 19 a jahar Jigawa

Askarawan Hisbah sun kama mata masu zaman kansu guda 19 a jahar Jigawa

Askarawan hukumar tabbatar da shari’an Musulunci a jahar, watau Hisbah ta sanar da kama wasu mutane 36 dake aikata munanan ayyuka a jahar, daga ciki akwai mata masu zaman kansu 19, maza yan giya 17.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa hisbah ta kama masu laifin ne yayin wani samame da ta kaddamar a gidajen karuwai da kuma gidajen shan barasa dake fadin jahar, inda tace ya kama kwalaben giya guda 647.

KU KARANTA: Goje ya bayyana abinda yasa Buhari ya umarci EFCC ta dakatar da shari’a da take yi da shi

Babban kwamandan Hisbah na jahar, Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuli a garin Dutse, inda yace sun kai wannan samame ne tare da hadin gwiwar jami’an Yansanda.

Kwamanda Dahiru ya jinjina ma kokarin da Yansanda suke yi a jahar da kuma hadin kan da suke basu wajen gudanar da ayyukansu, sa’annan ya yi kira ga jama’a dasu kauce ma aikata miyagun laifuka.

“Tuni mun gurfanar da wasu daga cikin masu laifin gaban kotu, yayin da muka mika wasu ga hukumar Yansanda domin su gudanar da bincike a kansu, tare da gurfanar dasu gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da binciken.

“Mun kama maza uku da mace daya a Jigawa, mun kama maza uku da mata hudu a Dutse, mun kama maza 11 da mata 14 a Gumel, sai kuma kwalaben giya 647 da babura 6 da muka kwace a yayin samamen.” Inji shi.

Jahar Jigawa na daya daga cikin jahohin Arewacin Najeriya dake dabbaka dokokin shari’ar Musulunci, sauran sun hada da Jahar Kano, Sakkwato da Zamfara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel