Shari’ar zaben shugaban kasa: Babu abinda ya hada Atiku da kasar Kamaru – Inji Balan gada

Shari’ar zaben shugaban kasa: Babu abinda ya hada Atiku da kasar Kamaru – Inji Balan gada

Wani Balan gada sarkin shaida, mai suna Mohammed Hayatu ya tabbatar ma kotun sauraron korafe korafen zabe cewa dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ba dan kasar Kamaru bane.

Hayatu ya bayyana haka a zaman kotun na ranar Talata, 16 ga watan Yuli, inda ya bayyana gaban kotun a matsayin shaida na 8 da Atiku Abubakar da PDP suka gabatar ma kotu, kuma yace mahaifar Atiku, Jada, dake jahar Adamawa bata zama cikin kasar Kamaru ba.

KU KARANTA: Jerin kamfanoni 34 da gwamnati ta baiwa kwangilar hakar danyen man fetir a Najeriya

“Ina sane da cewa akwai wani yankin jahar Adamawa daya taba zama a cikin kasar Kamaru, amma tabbas Jada bata taba zama cikin kasar Kamaru ba, akwai yankin kasar Kamaru da aka taba baiwa Najeriya a shekarar 1961, amma Jada bata cikin wannan yankin.” Inji shi.

Idan za’a tuna gabanin zaben 2019 ne shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu ya bayyana cewa Atiku Abubakar bad an Najeriya bane, dan kasar Kamaru ne, daga nan kuma abokan adawar Atiku suka dauka, har ma suka fi mai kora shafawa.

Shi dai Atiku an haifeshi ne a shekarar 1946 a kauyen Jada dake cikin karamar hukumar Ganye na jahar Adamawa, kuma nan ne matattaran yan kabilan Chamba, wanda a shekarar 1961 suka zabi su dawo cikin Najeriya daga kasancewa a yankin Arewacin Kamaru.

Binciken jaridar Premium Times ya nuna ko a shekarar da aka haifi Atiku Abubakar, yankin Jada na karkashin ikon kasar Turawan Kamaru ne, wanda bayan shawarar 1961 suka dawo Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel