Atiku ya yabawa gwamna Makinde da ya bayyana dukiyar da ya mallaka
Da yawa daga cikin al'umma masu fada a ji da kuma mashahurai a Najeriya, sun yabawa sabon gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da ya bayyana dukkanin dukiyar da ya mallaka a yayin karbar ragamar jagoranci.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya kasance daya daga cikin wadanda suka jagoranci jirgin yabawa gwamna Makinde kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.
A cewar Wazirin Adamawa, gwamna Makinde na jam'iyyar sa ta PDP ya cancanci yabo dangane da bayyana dukkanin dukiyar da ya mallaka da ko shakka babu hakan manuniya ce ta tabbatar da amincin sa da ya kamata ta zamto abun koyi ga sauran 'yan siyasa.
A ranar Litinin 15 ga watan Yuli, gwamna Makinde ya bayyanawa al'ummar kasar nan dukkanin dukiya da kadarori da ya mallaka. Wannan yunkuri da ya kwatanta, ya sanya shi a mataki daidai na tsohon shugaban kasa, marigayi Umaru Musa Yar'Adua.
Haka zalika, gwamna Makinde ya kasance a bisa mataki daidai da makamanci yunkurin da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo suka kwatanta na bayyana dukiyar su a shekarar 2015.
KARANTA KUMA: Nan ba da jimawa ba za mu bayar da amsar wasikar Obasanjo - ACF
Gwamna Makinde yayin bayyana tarin dukiyar da mallaka a ranar Litinin, ya kiyasta ta a kan kimanin naira biliyan 48 wadda ta hadar da gidaje, hannayen jari, kamfanoni da sauran kadarori na more rayuwa.
Baya ga Atiku, sauran wadanda suka yabawa gwamna Makinde a kan wannan yunkuri sun hadar da; kungiyar tsofaffin daliban jami'ar jihar Legas, hadimar shugaban kasa Buhari.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng