Masu uwa a gindin murhu: An damke makasan diyar shugaban kungiyar Yarbawa

Masu uwa a gindin murhu: An damke makasan diyar shugaban kungiyar Yarbawa

Kwanaki uku da kashe diyar shugaban kungiyar Yarbawa, Afenifere, Pa Reuben Fasoranti, hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da damke wadanda ake zargi da kashe Funke Olakunrin.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Ondo, Mista Femi Joseph, ya laburta hakan ne ranar Litinin.

A cewarsa, gamayyar jami'an tsaro masu sintiri ne suka afka cikin daji a Ore dake jihar Ondo inda suka samu nasarar damkesu.

Kakakin ya ce ba'a bayyana fuskokinsu ba amma za'ayi hakan ba da dadewa ba kuma ana cigaba da gudanar da bincike.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Gini mai hawa uku ya ruguzo kan jama'a a Jos

A bangare guda, Kungiyar Fulani Makiyayan ta Najeriya (MACBAN) ta yi Alla wadai tare da nesanta kan ta daga kisan Funke Olakunrin, diyar shugaban kungiyar 'yan kabilar Yoruba (Afenifere), Dattijo Reuben Fasoranti.

A wani jawabi da ta fitar ranar Asabar a Abuja, mai dauke da sa hannun sakarenta na kasa, Baba Ngelzarma, kungiyar MACBAN ta mika sakon ta'aziyya ga Fasorati a kan rasuwar diyarsa.

Ya ce marigayiyar ta mutu ne ranar Juma'a sakamakon harbinta da da wasu 'yan bidiga suka yi a kan hanyar Kajola zuwa Ore a jihar Ondo kamar yadda rundunar 'yan sanda ta bayyana.

Ngelzarma ya ce, "Muna mika sakon ta'ziyyar mu ga dangin marigayiyar."

Ya kara da cewa kungiyar MACBAN ta yi matukar mamakin yadda wani bangare na kafafen yada labarai da wasu marasa kishin kasa ke kokarin amfani da batun kisan marigayiya Funke domin rura wutar rikicin kabilanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel