Madalla: Wani mutumin kasar China ya amshi Musulunci a jihar Kano

Madalla: Wani mutumin kasar China ya amshi Musulunci a jihar Kano

Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa wani mutumin kasar China mai suna Leo ya mashi addinin Musulunci a jihar Kano.

Hakazalika Leo ya sauya sunansa zuwa na Musulunci inda ya zabi a sanya masa Aliyu, sunan daya daga cikin manyan sahabban annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Babban malamin nan na Musulunci, Sheikh Dr. Abdullah Usman Gadan Kaya ne ya musuluntar da Leo wanda ya kasance dan kasuwar kasar China

Madalla: Wani mutumin kasar China ya amshi Musulunci a jihar Kano
Madalla: Wani mutumin kasar China ya amshi Musulunci a jihar Kano
Asali: Facebook

An musuluntar dashi ne a masallacin Usman Bin Affan da ke Gadon Kaya a birnin Kano.

KU KARANTA KUMA: A yanzu bana iya zuwa mahaifana saboda masu garkuwa da mutane – Inji wani Sanata

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa hukumar alhazai ta kasa, NAHCON, ta sanar da cewa zuwa yanzu akwai mahajjatan Najeriya 6,396 da ta kai su kasar Saudiyya da nufin shirin fara Hajjin bana, a cikin kwanaki 5 da fara jigilar maniyyata aikin Hajji.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa ta yi wannan jigila cikin sawu 13 na jiragen sama, ta kara da cewa zuwa yanzu dai mahajjata daga jahohin Katsina, Legas, Kano, Kaduna, Kebbi da Kwara ne suka tashi zuwa kasa mai tsarki.

Kamfanonin jirage sama guda uku ne suke gudanar da aikin jigilar mahajjatan, da suka hada da MaxAir, Medview da kuma Flynas, bugu da kari a yanzu haka duka mahajjatan suna can anyi musu masauki a birnin Madina.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel