‘Yan barandan Jihar Zamfara sun tuba, sun mika makamansu ga ‘yan sanda

‘Yan barandan Jihar Zamfara sun tuba, sun mika makamansu ga ‘yan sanda

-'Yan barandan Zamfara sun fara bada makamansu ga jami'an 'yan sanda bayan an samu sulhu tsakaninsu da yan sintiri

-Kwamishinan 'yan sandan Zamfaran ne ya bamu wannan labari a yayin wata ganawa ta musamman da aka gudanar kan sha'anin tsaro a fadar Sarkin Anka

-Baqi ne suke kawo mana tashe-tashen hankula a yankinmu kamar yadda Sarkin Anka ya fadi a lokacin ganawar

Kwamishinan ‘yan sandan Zamfara, Usman Nagoggo ya bada labarin cewa ‘yan barandan jihar wadanda suka tuba sun fara bada makamansu ga hukumar ‘yan sandan jihar.

Nagoggo ya bada labarin cewa, tun bayan zaman sulhun da ya shirya wanda ya hada da ‘yan baranda da kuma kungiyar ‘yan sintiri a jihar, yanzu an samu zaman lafiya tsakanin kungiyoyin biyu da kuma fahimtar juna.

KU KARANTA:Zan sauke duk kwamishinan da ya gagara yin aikinsa – El-Rufa’i

Kwamishinan ya yi kira ga ‘yan baranda da cewa kada su ji tsoron bayyana kansu a duk lokacin da hukumar ‘yan sanda ta kira ganawa a kan zaman lafiya, inda yake basu tabbacin cewa ya riga da ya dakatar da duk wani yinkurin da kan iya kawo tashin hankali a jihar.

Nagoggo ya yi wannan jawabin ne a fadar Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad inda aka gudanar da wani zama na musamman kan sha’anin tsaro a yayin da Sarkin Anka ne ya jagoranci zaman.

Sarkin ya ce, “ tashe-tashen hankulan da su kayi ta addabar yankin na Anka a kwanakin nan ya kasance aikin baqi ne ba na ‘yan asalin jihar bane.”

Haka zalika, ya yi kira ga sauran masu rike da sarautun gargajiya da su ta shi tsaye wurin jaddada hanyoyin wanzar da zaman lafiya musamman a tsakanin ‘yan sintiri da ‘yan barandan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel