Shan kayan zaki na janyo cutar daji - Bincike

Shan kayan zaki na janyo cutar daji - Bincike

Wani binciken masana kimiyya na kasar Faransa ya nuna cewa shan zaki ciki harda ruwan yayan itatuwa na iya haddasa kamuwa da cutar daji.

An gano nasabar cutar dajin da shan ababen zakin ne bayan da aka gudanar da wani bincike da aka wallafa a mujallar British Medical Journal, wanda kuma ya duba sama da mutane 100,000 a cikin shekaru biyar.

An tattaro cewa tawagar masanan ta Jami'ar Sorbonne Paris Cite ta nuna cewa tasirin da sikari ke yi a cikin jini na iya zama dalilin alakar.

Sai dai kuma har iyau ba a tabbatar da sahihancin binciken ba kuma masana sun yi kira da a sake dubawa.

Wadannan ababe kamar yadda aka yi ikirari, Masanan sun bayyana su a matsayin lemukan da yawan sikarin da ke cikinsu ya wuce kashi biyar cikin dari.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Wasu 'yan sanda da aka tura su yaki masu garkuwa da mutane, sun buge da karbar cin hanci a hannun direbobi

Ciki har da ruwan 'ya'yan itatuwa (ko ba a kara masu sikari ba), lemukan kwalba da madarar da aka kara wa sikari da lemukan kara kuzari da shayi da kofi da aka kara wa sikari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel