An damke yan matasa 3 da sukayi garkuwa da karamin yaro a Kano (Hotuna)

An damke yan matasa 3 da sukayi garkuwa da karamin yaro a Kano (Hotuna)

Hukumar yan sandan Najeriya a ranar Alhamis ta bayyana cewa ta damke wasu yara uku da sukayi garkuwa da karamin yaro dan shekara 5, Ahmad Ado, kuma suka hallaka shi.

Hukumar a wata jawabin da kakakinta ya saki, Abdullahi Haruna, ya ce sun samu labarin cewa an yi garkuwa da yarin ranar Laraba, 10 ga watan Yuli.

Abdullahi Haruna ya ce sun samu labarin da yara masu garkuwa da mutanen sun bukaci milyan hamsin matsayin kudin fansa.

Kakakin yace sun damke babbban cikinsu, Ibrahim Ahmad, dan shekara 20 a matsayin babban wanda ya jagoranci wannan aika-aika.

Bayan gudanar bincike akansa, ya bayyana sauran abokan aikinsa, AbdulMajid Muhammad fa Musa Sanusi, masu shekaru 18 da haihuwa mazaunan Sheka Quarter, karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano.

Bayan binciken akansu, sun laburta cewa sai da suka baiwa yaron kwaya har ya mutu kuma suka birneshi cikin wata kango.

An damke yan matasa 3 da sukayi garkuwa da karamin yaro a Kano (Hotuna)
Kangon da suka birne yaron
Asali: Facebook

KU KARANTA: Zaben 2019: Yau Atiku zai gabatar da bidiyo matsayin shaida a kotu

A cewarsa: "Kwamishanan yan sanda, Ahmad Ilyasu, ya kai ziyara wajen tare da masana binciken gawa inda aka hako gawar yaron. An kaddamar da bincike kan gawar yaron kuma za'a gurfanar da matasan a kotu."

"Muna kira ga dukkan al'ummar jihar Kano su farga kan iyalansu saboda kulli yaumin yan baranda suna canza salonsu."

Daya daga cikin matasan ya bayyana yadda suka bukaci a basu milyan dari amma daga baya suka amince da dubu dari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel