Abokai 3 sun dura wa budurwa mai juna biyu ruwan omo don ta yi barin cikin da take dauke da shi

Abokai 3 sun dura wa budurwa mai juna biyu ruwan omo don ta yi barin cikin da take dauke da shi

An yanke wa wasu matasa guda uku hukuncin dauri a gidan yari bayan samun su da laifin lakada wa wata matashiya mai juna biyu dukan tsiya tare da dura mata ruwan omo a baki domin ta yi barin juna biyun da ta ke dauke da shi.

Matashiyar, mai shekaru 17, ta sha ukuba a hannun matasan ne bayan ta ki amincewa da zubar juna biyun da take dauke da shi kamar yadda saurayinta, Harief Pearson, ya bukata, kamar yadda mai gabatar da kara ya sanar da kotun Harrow Crown.

Wani bincike da aka gudanar a wayar hannun saurayin, mai shekaru 22, ya nuna cewar ya yi binciken hanyoyin zubar da juna biyu a yanar gizo.

Lamarin ya faru ne sati biyu kafin Kirsimeti yayin da matashiyar ta ziyarci Pearson a gidansa da ke Harlesden lardin Scotland a yammacin London ta kasar Ingila.

Matashiyar ta so barin gidan Pearson bayan sun tafka mahawara a kan ta ki amincewa da bukatarsa ta zubar da juna biyun da take dauke da shi, wanda kuma shine ya yi mata.

Duk wannan takaddama da ke matashiyar mai juna Pearson ke tafka wa, na faruwa ne a gaban wata matashiya mai shekaru 16 wacce ke tare da shi kafin budurwarsa mai juna zo gidan.

Ana cikin haka ne sai ga wani abokin Pearson mai suna Mckenna, mai shekaru 22, ya shigo gidan.

DUBA WANNAN: Yadda wata matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta suka kashe yayan ta

Matashiyar da ke tare da Pearson da Mckenna ne suka hau jibgar mai juna biyun bisa tunanin hakan zai saka juna biyun da ta ke dauke da shi ya zube. Hakan ta faru ne bayan Pearson ya fita daga dakin da dukkansu ke tare.

Bayan Pearson ya dawo ne sai ya tambayi budurwar ko juna biyun da ta ke dauke da shi ya zube sakamakon dukan da ta sha, amma sai ta ce ita ma ba ta sani ba. A nan ne Pearson ya bukaci abokan na sa su dakata da dukan mai juna biyun tare da jika garin Omo wnda suka dura mata ta karfi don cikinta ya zube.

Mckenna ne ya kira motar asibiti domin ta dauki matashiyar bayan Pearson ya yi mata barazana da kurarin daukan mataki mai tsanani idan ta sake ta sanar da abinda suka yi mata.

Sai dai, barazanar ba ta yi tasiri a kan matashiyar ba domin kuwa ana zuwa asibiti ta sanar da likitoci, su kuma suka sanar da 'yan sanda.

An kama Pearson da matashiyr a ranar 12 ga watan Disamba, yayin da aka kama Mckenna bayan wata guda saboda ya shiga wasan buya da jami'an tsaro.

Jaririn da ke cikin matashiyar ya tsira, don kuwa ta haife abinta lafiya, kamar yadda jaridar birnin Landan ta wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel