Adadin al'ummar Najeriya ya kai 190m - NPC

Adadin al'ummar Najeriya ya kai 190m - NPC

Hukumar kidaya ta kasa, NPC, National Population Commission, ta ce a halin yanzu kiyasi ya yi nuni da cewa adadin al'ummar Najeriya ya kai kimanin mutane miliyan 190.

Shugaban hukumar NPC na kasa, Dakta Ghali Isma'il, shi ne ya bayar da wannan shaida cikin wani furuci yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata 9, ga watan Yulin 2019.

Dakta Isma'ila yayin bayyana wannan kiyasi ya ce akwai bukatar hukumar ta tabbatar da ainihin adadin al'ummar kasar nan wajen sake gudanar da kidayar al'ummar Najeriya nan ba da jimawa ba.

Ya ke cewa, duba da hasashe da kuma nazari mai zurfin gaske da hukumar NPC ta gudanar, kiyasin ta yayi nuni da cewar adadin al'ummar kasar nan ya kai kimanin mutane miliyan dari da casa'in.

Sabanin sakamakon kiyasin da ta fitar watanni uku da suka gabata, majalisar dinkin duniya ta yi hasashen cewa akwai kimanin mutane miliyan 201 a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Hadin kai ne kadai zai kawo karshen rashin tsaro da kabilanci a Najeriya - Osinbajo, Tinubu

Babban jagoran hukumar ya jaddada muhimmancin sake gudanar da kidayar al'ummar kasar nan wanda a cewar sa hakan zai yi tasirin gaske musamman a fannin tsaro da kuma tattalin arziki na kasa.

Hukumar NPC yayin kidayar al'ummar Najeriya da ta gudanar tun a shekarar 2006 da ta gabata, ta tabbatar da adadin mutane 140,431,790, inda jihar Kano da kuma Legas suka kasance a kan sahu na gaba ta fuskar yawan adadin al'umma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel