Zan farfado da duka matatun man Najeriya 4 kafin 2023 – Mele Kyari

Zan farfado da duka matatun man Najeriya 4 kafin 2023 – Mele Kyari

Sabon shugaban hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC, Mele Kyari ya dauki sabon alkawari game da aikin gyaran matatun man Najeriya guda hudu, inda yace zai farfado dasu dukansu, inji rahoton Tribune.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kyari ya bayyana haka ne yayin da yake karbar ragamar mulki daga shugaban hukumar mai barin gado, Kachalla Maikanti Baru, wanda ya sauka daga shugabancin hukumar a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli sakamakon kaiwa shekarun ritaya.

KU KARANTA: Babban Faston Najeriya ya yi kira ga Buhari ya yi murabus daga kujerar shugaban kasa

Malam Kyari yace zai tabbata dukkanin matatun man fetir na Najeriya sun fara aiki zuwa shekarar 2023, sa’annan ya kara da cewa ba zai lamunci cin hanci da rashawa ba, don haka zai kawar da duk wasu ayyukan rashawa daga hukumar.

“Zamu yaki cin hanci da rashawa, zan yi aiki hannu da hannu da dukkanin masu ruwa da tsaki a hukumar NNPC domin tabbatar mun cimma wannan buri da muka sa gaba, ina sane da nauyin dake tattare da shugabancin NNPC, ko ba komai na san zan tsaya a gaban ubangijina na bada bahasin yadda na tafiyar da hukumar.

“Zamu gina kamfanin nan kamar yadda sa’o’insa suke a duniya, ba wai ina nufin ba zamu tafka kurakurai bane, amma dai ba zamu tafka kurakurai da gangan ba. Ina sanar da iyalina da dangina, idan kuka amshi kyauta daga hannun wani mutumi, toh ku sani ba ni aka ba ba.

“Don haka duk masu tunanin zasu iya bi ta hannun yan uwana, su sani, yan uwana ba zasu taba iya juyani ba. Zamu farfado da matatun man Najeriya guda hudu kafin karewar wa’adin mulkin shugaba Buhari, zamu tabbatar da Najeriya ta daina shigo da tataccen man fetir.” Inji shi.

Daga karshe Kyari ya yi jinjina ta musamman ga Maikanti Baru, tare da yaba mai bisa rawar daya taka wajen gyara al’amura a NNPC, sa’annan ya gode ma shugaba Buhari daya bashi wannan dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel