Kotu: Kuskure ne INEC ta ce bata da rumbun tattara sakamakon zabe - Shaidar Atiku

Kotu: Kuskure ne INEC ta ce bata da rumbun tattara sakamakon zabe - Shaidar Atiku

Mista Peter Uzioma Obi, shaida na biyu da jam'iyyar PDP da dan takarar ta a zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar, suka gabatar a gaban kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa, ya ce kuskure ne hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta ce ba ta da rumbun tattara sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu.

Obi ya bayyana hakan ne yayin da aka kira shi a gaban kotun a matsayin shaida a karar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da INEC ta bayyana shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da jam'iyyar APC a matsayin wadanda suka yi nasara.

Obi, wanda ya bayyana cewa ya yi aikin zabe a matsayin RATECH (Registration Area Technician) a jihar Ribas lokacin zabukan shekarar 2019, ya bayyana cewa INEC ta basu horo a kan yadda zasu aika mata sakamakon zabe zuwa babban rumbunsu na tattara sakamako.

Shaidar na wadannan kalamai ne yayin da ya ke amsa tambayoyin lauyan hukumar zabe, Yunus Usman (SAN), a gaban kotun.

"Ba kai ne ya kamata ka aika sakamakon zabe ba saboda ba kai ne 'presiding officer' ba," Usman ya fada wa Obi.

Da ya ke bashi amsa, Obi ya ce, "ba haka bane ranka ya dade. INEC ta bamu horo a kan yadda za a aika sakamakon zabe. Ba ni ne 'presiding officer' ba. Ni ne kwararre da ke kula da na'ura a mazabar da na yi aiki. INEC ce kuma ta bani horon sanin makamar aiki tare da ragowar ma'aikatan ta na wucin gadi."

Da ya ke amsa tambaya daga Cif Wole Olanipekun (SAN), lauyan shugaba Buhari, Obi ya bayyana cewa bashi da masaniyar dokokin da INEC ta yi amfani da su a zaben shugaban kasa, sannan ya kara da cewa amma akwai takarda mai dauke da ka'idojin aikinsa na RATECH, wanda INEC ta bashi horo a kai.

Da ya ke amsa tambayoyi daga Lateef Fagbemi (SAN), lauyan jam'iyyar APC, Obi ya ce duk da bai yi aiki a matsayin PO (presiding Officer) ko APO (Assistant Presiding Officer) ba, sanannen abu ne ga duk wanda ya yi aikin zabe na wucin gadi cewa INEC ta bukaci a ke aika mata da sakamakon zabe zuwa babban rumbunta na tattara sakamakon dukkan zabukan da aka kammala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel