Najeriya kasa ce mai fuska biyu ce, yayinda Kudu ke cigaba, Arewa na cibaya - El-Rufai

Najeriya kasa ce mai fuska biyu ce, yayinda Kudu ke cigaba, Arewa na cibaya - El-Rufai

-Gwamna Nasir El-Rufai ya janyo hankalin 'yan arewa a kan matsalar dake damun yankin ta rashin cigaba da kuma fama da talauci

-Gwamnan yayi wannan kiran ne yayin da ya halarci wani taro na musamman da aka shirya a jihar Kaduna domin 'yan arewacin Najeriya

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a ranar Asabar ya bayyana Najeriya a matsayin kasa wadda ke da fuskoki guda biyu, inda ya ce akwai bangaren Kudanci wanda ke cigaba da kuma bangaren Arewaci wanda ke fama da jahilci, talauci da kuma rashin cigaba.

A cikin jawabin gwamnan ya yi kokarin kamanta Arewacin Najeriya da kasar Afghanistan wadda yaqi ya dai-daita.

KU KARANTA:Buhari ya tashi daga Abuja zuwa Nijar domin halartar taron AU

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a wani taro na musamman da kungiyar Northen Hibiscus ta shirya domin ‘yan Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya fadi cewa, domin magance matsalar da yankin Arewa ke fama da shi ya zama wajibi sai gwamnonin jihohin arewa 19 sun hada hannu wuri daya.

Ga abinda gwamnan ya fadi a kalamansa: “ Idan muka duba kididdiga zamu samu cewa Najeriya kasa tamkar wadda bata da wata matsala. Amma idan aka raba kasar zuwa jihohi ko kuma bangarori daban-daban, sai ka samu cewa Najeriyar fuska biyu gare ta.

“ Akwai bangaren Arewa dake fama da jahilci, talauci da rashin cigaba sannan kuma akwai yankin Kudu dake da ilimi, arziki da kuma cigaba. Ya zama wajibi mu fadi gaskiya, shin ko ka taba tambayar kan ka dalilin da ya sa Arewacin Najeriya a fannin cigaba yake tamkar kasar Afghanistan, inda har a yau yaqi ake?

“ Mun fi kowa yawan mutane masu fama da talauci a duniya, kuma akasarinsu suna arewa ne. Haka zalika Najeriya ce ta fi ko wace kasa yawan yara marasa zuwa makaranta kuma yawancinsu daga arewa suka fito.

“ A don haka ya zama wajibi gare mu a matsayinmu na shugabanni mu rika tattauna ina zamu bi domin samun mafitar wannan al’amari dake damun mu. Ana kallon yankin mu a matsayin ci ma zaune, amma alhamdulillahi wanda ya fi kowa kudi a Najeriya dan arewa ba kudu ba.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel