Da yiwuwan Sanata Elisha Abbo ya kwana a kurkukun yan sanda yau - Yan sanda

Da yiwuwan Sanata Elisha Abbo ya kwana a kurkukun yan sanda yau - Yan sanda

Da yiwuwan sanata Elisha Ishaku Abbo ya kwana a kurkukun yan sanda yau bayan mika kansa ga hukumar domin bincike kan zargin da ake yi masa na cin zarafin wata matar aure.

Mun kawo muku rahoton cewa kwamishanan yan sandan birnin tarayya, Bala Ciroma, ya tabbatar da cewa Sanata Abbo ya mika kansa ga hukumar bayan ta bukaci ganinsa a ranar Laraba.

Karidar Premium Times ta bada rahoton cewa sanatan wanda ya mika kansa yana hedkwatan hukumar yan sandan Abuja misalin karfe 8:15 na daren yau Alhamis bayan kwashe sa'o'i hudu a ofishin.

Kwamishanan yan sanda Ciroma ya ce da yiwuwan ba za'a saki Sanata Abbo da daren nan ba muddin bai cika sharrudan beli ba.

Amma kwamishanan bai bayyana ko za'a gurfanar da shi a kotu ba ko a'a.

KU KARANTA: Abinda shugabannin tsaro suka tattauna da Shugaba Buhari

Jama'a sun hurawa hukumar yan sanda wuta kan su tabbatar da cewa na gurfanar da sanatan a kotu inda suke cewa hakurin da ya bada kadai ba zai isar ba. Ya kamata a hukuntashi saboda hakan ya zama darasi ga wasu masu halin dukan mata.

A daren Laraba, Sanata Abbo, ya yi hira da manema labarai inda ya baiwa al'ummar Najeriya hakuri kan abinda yayi na cin zarafin matar aure wanda ya bayyana karara a faifan bidiyo.

Har yanzu, matar auren da ya buga, Bibra, bata furta magana daya ba har yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng