Magidanci ya kwankwadi 'sniper' bayan ya kama matarsa turmi da tabarya da tsohon saurayin ta

Magidanci ya kwankwadi 'sniper' bayan ya kama matarsa turmi da tabarya da tsohon saurayin ta

Wani magidanci mai shekaru 51 ya jefa iyalinsa cikin damuwa bayan ya kwankwadi wani maganin kashe kwari mai karfin gaske (sniper) saboda ya dawo daga aiki ya kama matarsa turmi da tabarya ta na lalata da tsohon saurayinta.

Magidancin, dan asalin kasar Zimbabwe, ya kashe matar ta sa sannan ya gaggauta shan maganin kwari.

Rahotanni sun bayyana cewa magidancin mai suna Simbarashe Chidaushe, mazaunin garin Gokwe, ya yi amfani da gatari wajen kashe matar bayan ya kama ta dumu-dumu ta na cin amanarsa da wani mutumin, sannan ya yi kokarin kashe kansa ta hanyar shan maganin kwari.

Magidanci ya kwankwadi 'sinper' bayan ya kama matarsa turmi da tabarya da tsohon saurayin ta
Magidanci ya kwankwadi 'sinper' bayan ya kama matarsa turmi da tabarya da tsohon saurayin ta
Asali: Twitter

Magidanci ya kwankwadi 'sinper' bayan ya kama matarsa turmi da tabarya da tsohon saurayin ta
Magidanci ya kwankwadi 'sinper' bayan ya kama matarsa turmi da tabarya da tsohon saurayin ta
Asali: Twitter

Yanzu haka Chidaushe na can asibitin yankin Gokwe inda likitoci ke kokarin ceto lafiyarsa bisa 'sa idon' jami'an 'yan sanda da ke gadin dakin da aka kwantar da shi.

Majiyar mu ta bayyana cewa Chidaushe, dan asalin kauyen Njele, ya kama matarsa, Chiedza Mpofu, na saduwa da saurayinta bayan ya yi wata dawowar bazata daga wurin aikinsa da ke wani gari kusa da garin Gokwe da yake zaune da iyalinsa.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Na kashe mutane fiye da 50, na samu kudi kusan miliyan N700 - Mai garkuwa da mutane

Jami'in dan sanda, Insifekta Goko, ya ce wasu mutanen gari ne suka kai rahoton faruwar lamarin tare da bayyana cewa an kai gawar Mpofu asibitin da Chidaushe ke samun kulawa.

Ya kara da cewa jami'an 'yan sanda na cigaba da 'sa ido' a dakin da aka kwantar da Chidaushe kuma da zarar ya samu lafiya za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel