Dalilin da ya sa na daina zuwa yin jaje Zamfara – Yariman Bakura

Dalilin da ya sa na daina zuwa yin jaje Zamfara – Yariman Bakura

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura ya yi jawabi a kan dalilin da ya sa bai damu da zuwa yiwa mutanen jihar jaje akan yawan kashe-kashen da yan bindiga ke kaddamarwa.

Yariman Bakura, wanda ya kasance gwamnan farar hula na farko a jihar daga 1999 zuwa 2007 kuma sanata har zuwa 2019, ya bayyana cewa akwai wasu muhimman abubuwan da suka fi zuwa jaje wanda ya kamata shugabanni su mayar da hankali a kai.

"Na fara zuwa sai na ga abu ne da ake yi kullum, sai na koma ina ba da shawara kan matakan da ya kamata a dauka," a cewar Yarima.

A jawabinsa, wacce ya tatattauna batutuwan da suka shafi tsaro da siyasa da kuma shari'a, ya bayyana cewa zuwansa jaje ba zai kawo karshen matsalar tsaro a jihar ba.

Jihar Zamfara na cikin jihohin arewa maso yammacin kasar da ake yawan samun kashe-kashe da sace-sacen mutane, lamarin da ke jefa mazauna yankin cikin fargaba da raba wasu da gidajensu.

KU KARANTA KUMA: Mataimakin Dankwambo ya karyata rade-radin karban kyautar mota daga jigon APC a Gombe

Wasu 'yan Najeriya, musamman ma a jihar, sun dade suna alakanta matsalolin da rashin samun jagoranci nagari tun bayan dawowar mulkin damokradiyya.

Kuma Sanata Yarima, wanda shi da abokan siyasarsa suka shafe shekara 20 suna mulkar jihar, ya amince cewa talauci ne ya jefa jihar cikin halin da take ciki a yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng