Tonon asiri: Gwamnan Borno zai fallasa wadanda suka ci N2bn na tallafin sana'o'i
-Gwamnan jihar Borno zai bayyana sunayen wadanda suka yi sama da kudin CBN na bashin tallafawa masu kananan sana'o'i
-Babagana Umara ya fadi wannan maganar ne yayin da tawagar ma'aikatan CBN reshen jihar Borno ta kai masa ziyara a ofishinsa
-A shekarar 2015 ne Babban Bankin Najeriya wato CBN ya bai wa gwamnatin jihar bashin N2bn domin samar wa masu kananan sana'o'i da tallafi
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara ya ce, gwamnatinsa zata bankado sunayen mutanen da suka yi sama da naira biliyan biyu da CBN ta bai wa jahar bashi domin samar da tallafi ga masu kananan sana’o’i.
Gwamnan ya yi wannan furucin a ranar Laraba yayin da yake karbar bakoncin tawagar ma’aikatan CBN reshen jihar Borno wadanda suka kawo masa ziyara a ofishinsa.
KU KARANTA:Lawan ya roki Kungiyar kwadagon Najeriya da ta janye maganar yajin aiki
Tawagar ta CBN a yayin da take tsokaci ga gwamnan kan shiyyoyin da bankin zai iya taimakon jihar Borno musamman domin habbaka tattalin arziki, ta nuna rashin jin dadinta kan rashin amfani da bashin N2bn wanda aka bayar a shekarar 2015 ta hanyar da ta dace.
A cewar shugaban CBN reshen jihar Borno, Lawal Tijjani, “babu ko mutum guda da ya dawo da wannan bashin duk da cewa lokacin da aka shata domin biyan bashin ya riga da ya wuce.”
Binciken da jaridar Premium Times ta yi ya bayyana mana cewa, a shekarar 2015 gwamnatin jihar Borno ta karbi bashin naira biliyan biyu daga CBN domin samar da tallafi ga masu kananan sana’o’i a jihar.
Wata majiya wacce keda sani kan yadda wannan lamari ya auku ta shaida mana cewa, “sam ba a bi tsarin karbar bashin bisa ka’ida ba. Manya-manyan jami’an gwamnati, masu rike da sarautun gargajiya da kuma hamshakan ‘yan kasuwa su ne suka rika kewayawa suna karbar wannan bashin.”
Har wa yau, majiyar ta sake sanar da Premium Times cewa “da yawa daga cikin wadanda suka karbi bashin, ba wai sun sanya shi cikin kasuwanci bane, kawai hidimar gabansu sukayi da kudin."
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng