Iran za ta inganta karfin makamashin nukiliyarta, inji Shugaban kasar

Iran za ta inganta karfin makamashin nukiliyarta, inji Shugaban kasar

-Kasar Iran ta cije a kan bakarta na bunkasa makamashin Nukiliya kamar yadda Shugaban kasar, Hassan Rowhani ya shaida mana

-Rowhani ya ce kasarsa za ta fara wannan aikin ne a ranar Lahadi 7 ga watan Yuli inda zasu daga karfin makamashin nukilayar ya haura 3.67% kamar yadda yake a halin yanzu

-Rahotanni sun nuna cewa akwai yiwuwar kungiyar Tarayyar Turai za ta gana da qasar Iran kafin 7 ga watan Yuli domin samar da masalaha a kan lamarin

Kasar Iran za ta inganta karfin makamashin nukiliyarta na uraniyum wanda za ta fara gudanar da aiki a kansa daga ranar Lahadi, a cewar Shugaba Hassan Rowhani.

Rowhani ya yi karin haske a kan lamarin, inda ya ce wannan shi ne sashe na biyu daga cikin tsarin sarrafa makamashin nukuliyar wanda aka yi yarjejeniya tare da sauran kasashen duniya tun a shekarar 2015.

KU KARANTA:Hajjin bana: Kasar Saudiya ta fito da sabon tsarin samar da biza ga mahajjata

“ A ranar 7 ga watan Yulin 2019, makamashin mu na uraniyum zai samu kari a kan 3.67%”, kamar yadda Rowhani ya shaidawa ‘yan majalisarsa yayin da suke ganawa a ranar Laraba.

Jawabin Shugaban yazo daidai ne da tsarin da aka gina a watan Yuni a Tehran babban birnin kasar Iran. A watan Yuni, kasar Iran ta yi ikirarin saba wa yarjejeniyar ta hanyoyi guda biyu, in dai har sauran kasashen dake da hannu a yarjejeniyar, ba su kawo dauki a kan matsalolin tattalin arziki ba.

Na farko an riga da an samu kammala shi ranar Litinin, yayin da hukumar kasa da kasa mai kula da nukiliya ta ruwaito cewa ma’adanar nukiliyar kasar Iran ta wuce kilo 300 kama yadda yarjejeniyar ta gindaya.

Abu na biyun kuwa shine, zancen da Rowhani ya sake jaddadawa a ranar Laraba inda yake cewa, kasarsa na shirin sake inganta karfin makamashin nukilayar ta yadda zai haura 3.67%.

A shekarar bara ne dai kasar Amurka ta fita daga cikin yarjejeniyar shekarar 2015 tare da sanya ma Iran takunkumin tattalin arziki.

A halin yanzu dai, an zuba idanu domin ganin yadda tattaunawa wadda ake sa ran kasar Iran da Kungiyar Tarayyar Turai za suyi kafin ranar 7 ga watan Yuli, 2019 za ta kasance.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng