Da dumi dumi: El-Rufai ya sanar da sunayen sabbin kwamishinoni guda 11

Da dumi dumi: El-Rufai ya sanar da sunayen sabbin kwamishinoni guda 11

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya mika ma majalisar dokokin jahar sunayen mutane goma sha daya da yake muradin nadasu kwamishinoni, domin majalisa ta tantancesu.

Legit.ng ta ruwaito kaakakin majalisar dokokin jahar, Aminu Shagali ne ya bayyana haka yayin da ya bayyana ma takwarorinsa takardar da gwamnan ya aiko masa dake kunshe da sunayen kwamishinonin a ranar Laraba, 3 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kwalejin kimiyyar lafiya

Ga jerin sunayen kwamishinonin kamar haka:

Ja’afaru Sani – Ma’aikatan kananan hukumomi

Idris Nyam – Ma’aikatan kasuwanci, kirkire kirkire da kimiyya

Shehu Muhammad – Ma’aikatan ilimi

Husaini Garba – Ma’aikatan muhalli da ma’adanan kasa

Kabiru Mato – Ma’aikatan wasanni

Balaraba Aliyu-Inuwa – Ma’aikatan ayyuka

Samuel Aruwan – Ma’iakatan tsaron cikin gida da al’amuran cikin gida

Fausat Ibikunle – Ma’aikatan gidaje da cigaban birane

Muhammad Saidu – Ma’aikatan kudi

Hafsat Bello – Ma’ikatan walwalar jama’a da cigaban al’umma

Aisha Dikko – Ma’aikatan shari’a.

Kammala karanto sunayen keda wuya, said an majalisa Samuel Ubankato ya nemi majalisar ta gayyaci mutanen da El-Rufai ya aiko sunayensu dasu bayyana gaban majalisar a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli domin su fara tantancesu, na da nan dan majalisa Mohammed Ahmed ya goyi bayan hakan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng