Ashe an hana Sanata Elisha shiga makaranta saboda cutar Kanjamau da yake dauke dashi

Ashe an hana Sanata Elisha shiga makaranta saboda cutar Kanjamau da yake dauke dashi

Rahoton Daily Nigerian ya bayyana cewa Sanata Elisha Ishaku Abbo, dan majalisar dattawan da ake zargi da dukan wata mata a shagon siyar kayayyakin tsiraici a Abuja, yana dauke da cutar Kanjamau.

Saboda wannan ciwo da yake fama dashi kwalejin horon sojin ruwa dake Onne, Port Harcourt ta hanashi admisho a shekarar 2004.

Elisha Abba, wanda ke wakiltar mazabar Adamawa ta Arewa ya bayyana a wani bidiyon leken asiri inda aka ganoshi yana marin wata mata dake kokarin bashi hakuri a shagon.

Wannan bidiyo da aka dauka ranar 11 ga Mayu, 2019, ya faru ne gaban jami'in dan sanda amma ko uffin bai ce ba, bal taimakawa yayi wajen cin zalin matar.

KU KARANTA: Za a sake shiga wahalar man fetur – IPMAN

A ranar 9 ga Febrairu, 2004, Elisha Ishaku ya kai karar kwalejin horon sojin ruwa dake Onne, Port Harcourt kotu kan hanashi shiga makarantar duk da cewa ya ci jarrabawar shiga saboda dalilin cewa yana fama da mugun cuta.

A karar da ya shiga, inda mataimakin shugaban kungiyar lauyoyin Abuja, Barista Jude Okeke, ya wakilcesa a babbar kotun tarayya dake Abuja, Sanata Ishaku ya bukaci kotun ta yanke hukuncin cewa wannan abu da kwalejin tayi na hanashi shiga saboda lafiyarsa a matsayin take hakkinsa na dan Adam kuma hakan ya sabawa dokar kasa.

Amma ba'a san yadda suka kare ba.

A bangare guda, Shugaba majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya kafa kwamiti na musamman domin bincike cikin bidiyon da ya yadu a kafofin ra'ayi da sada zumunta wanda ke nuna sanata Elisha Ishaku, mai wakiltar Adamawa ta kudu yana dukan mace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng