Babbar magana: Matar wani alkali a Gombe ta kashe yaron alkalin a kan idonsa
- Matar wani Alkali a jihar Gombe ta kashe wani yaron alkalin a lokacin da alkalin yake gida
- Matar tayi amfani da wuka ta cakawa yaron a kahon zuci, lokacin da yaron ya dawo daga aiken da alkalin yayi masa
- Mahaifiyar yaron ta bayyana cewa baza su taba yafewa ba, tunda aka kashe mata danta guda daya tilo
Matar alkalin kotun majistire Mai Shari'a Aliyu Abubakar, dake garin Nafada a karamar hukumar Nafada cikin jihar Gombe.
Matar mai suna Fatima Ardo Chindo Abubakar ta kashe dan gidan alkalin ta hanyar soka masa wuka a kahon zuci, a lokacin da alkalin yake gida.
Kamar yadda jaridar Aminiya ta lalubo, marigayin mai suna Hamza Adamu wanda aka fi sani da Awilo, ya mutu ne yayin da mai gidansa, Mai Shari'a Aliyu Abubakar yayi kiransa a waya ranar Lahadin da ta gabata.
Alkalin ya aiki Awilo akan yaje ya siyo masa Indomie, ruwan gora na Faro, da Maltina ya kawo masa.
Awilo na shigowa matar alkalin ta tare shi cikin fushi take tambayarsa menene a cikin ledar, sai yake fada mata alkali ne ya aikeshi, sai ta hau masifa cewa dama dashi ake hada baki ana so a kashe mata aure.
Matar ta shammaci Awilo ta kama hannunsa ta gartsa masa cizo, shi kuma da yaji zafi sai ya ture ta, ashe akwai wuka a jikinta, cikin gaggawa ta dauko wukar ta daba masa a kahon zuci, take ya fadi a gurin.
KU KARANTA: Tashin hankali: Wani matashi ya cakawa abokinshi kwalba a kahon zuci akan guntuwar giya
Jin karar yasa makwabta suka shigo gidan domin ganin abinda ke faruwa sai suka ga Awilo kwance cikin jini ga kuma matar alkali a kanshi da wuka a hannu.
Cikin gaggawa suka sanar da hukumar 'yan sanda, inda aka garzaya da Awilo asibiti, kafin su karasa rai yayi halinsa.
Da wakilan Aminiya suka gana da iyayen marigayin, mahaifiyar yaron mai suna Hajiya Aisha Manzo da aka fi sani da Hajja Manja ta ce basu yafe ba, kuma suna jira suga yadda shari'a zata kasance akan matar alkalin da ta kashe dansu a gabansa ba tare da yace komai ba.
Mahaifiyar Hamza ta bayyana cewa: "Hamza shine da guda daya da Allah ya bani, shekararsa 40 da haihuwa, tunda na haife shi Allah bai sake bani wata haihuwar ba, yaya za ayi a kashe mini shi kuma baza a hukunta wacce ta aikata laifin ba."
An yi kokarin jin ta bakin alkalin, mijin matar da tayi wannan aika-aika amma lamarin ya faskara.
Sai dai kuma mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, DSP Mery Obed Malum, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa har yanzu suna gabatar da bincike akan lamarin
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng