Jerin sunayen Jakadun Najeriya da suka yi sama da fadi da biliyoyin kudi bayan sunyi murabus

Jerin sunayen Jakadun Najeriya da suka yi sama da fadi da biliyoyin kudi bayan sunyi murabus

A cikin watanni shida, Janairu zuwa Yuni 2019, gwamnatin Najeriya ta biya sama da naira biliyan 7 a matsayin alawus ga jakadodi 26 wadanda sun dade da ritaya amma suka ci gaba da aiki wuraren a kasar waje ba bias ka’ida ba.

An tattaro cewa kudaden masu biyan haraji da aka kashe wajen daukar dawainiyar wadannan jakadu 26 a watanni shida na 2019 ya tasar ma dala miliyan 20 sama da naira biliyan 7 kenan.

SaharaReportrers ta saki sunayen jakadun Najeriya da suka mori miliyoyin dala a matsayin alawus duk da sun yi ritaya. A bisa ga sunayen, wasu daga cikin jakadun sun yi ritaya tun a farkon Nuwamban 2018.

Sunayen jakadun masu ritaya sun hada da: Amb. AG Bala (Hong Kong), Amb. Jane Ndem (Romania), Amb. Salisu Umaru (Senegal), Amb. Martin Cobham (Venezuela), Amb. E.P Duchi (Israel), Mr. Amedu Ode (Singapore). Sauran sun hada da Amb. HT Balogun (Indonesia), Amb. AA Sonaike (Philippines), Amb. Baba Garba (Morroco), Amb. Ibrahim Isah (Cote D'Ivoire), Amb. Vivian Okeke (Austria), da dai sauransu.

Wadannan jakadun sun ci gaba da karban albashi a dalar Amurka nasu, na matansu, da kuma na hadimansu wanda ya kai kimanin dalar Amurka miliyan 3.4 duk wata.

Wata majiya ta fadar Shugaban kasa ta bayyana yadda Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari, ya soke umurnin Shugaban kasar na dawo da jakadun masu ritaya Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Aiki ga mai yin ki: Gbajabiamila na so a gabatarwa da majalisar dokoki kasafin kudin 2020 a watan Satumba 2019

Majiyar tace ministan harkokin waje ya aika wasika zuwa ga jakadun da abun ya shafa sannan ya nemi su mika mulki ga babban jami’in daiflomasiyya a kasashen da suke. “Yan kwanaki bayan haka, sai Kyari ya aika sammaci ga Onyeama tare da Amb. AR Abubakar, zuwa Villa inda suke bukaci ya janye umurnin da Shugaban kasar ya bayar."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng