Ya kamata a fara biyan Ma’aikatan Najeriya sabon albashi - IPAC

Ya kamata a fara biyan Ma’aikatan Najeriya sabon albashi - IPAC

Mun samu labari cewa majalisar IPAC ta jam’iyyun Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta hanzarta da maganar karin albashi domin ma’aikata su samu sa’ida wajen sha’anin rayuwa.

Shugaban IPAC na reshen jihar Legas, Shakirudden Olofin, ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da manema labarai a Garin Legas. An yi wannan zantawa ne a Ranar 30 ga Watan Yuni, 2019.

Shakirudden Olofin ya ke cewa ma’aikatan kasar nan sun cancanci a kara masu albashi domin wannan ne zai kawo masu saukin rayuwa. A cewarsa rayuwa ta yi tsada matuka yanzu a Najeriya.

Olofin ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a game rattaba hannu da ya yi kan kudirin sabon karin albashi a Najeriya inda ya nemi a yi maza a fara dabbaka wannan tsari a fadin kasar.

“Gwamnatin tarayya ta Buhari ta yi kokari wajen aminewa da karin albashi da kuma ratttaba hannu a kan dokar.”

KU KARANTA: Matasan APC na Gombe sun fadawa Buhari wadanda za a ba mukami

“To sai dai tun Watan Afrilu da a ka sa hannu a kan wannan doka, har yanzu a na ta samun cikas iri-iri yau da gobe. Kuma a ganina, gwamnati ba tayi wa ma’aikata adalci ba” Inji Olofin.

Shugaban na IPAC ya ce: “Tsadar rayuwa ya nunku a cikin shekaru 6 da su ka wuce, amma har yanzu wasu Ma’aikata su na tashi ne da N18,000 a wata.”

S. Olofin ya cigaba da cewa “Duk da N30, 000 din da a ka sanya bai dace da wannan hali da a ke ciki ba. Amma dai ya kamata soma biyan wannan kudi."

Inda a ke samun kalubalen shi ne a game da ma’aikatan da ke karbar albashin da ya haura N30,000 a halin yanzu. IPAC ta ce ya kamata wannan karin albashi ya shafi kowane ma’aikaci a kasar.

”A kasar da ‘Yan Majalisa da manyan ‘yan siyasa su ke tashi da miliyoyi da sunan alawus da albashi, zai zama rashin tausayi a ce ba za a karawa wasu albashi ba.” Olofin ya nemi Buhari ya gyara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng