Wuya ba dadi: Yan ta'addan Katsina sun roki gafara

Wuya ba dadi: Yan ta'addan Katsina sun roki gafara

-Wasu gungun yan ta’adda a jihar Katsina sun roki gwamna Masari da ayi sasanci kuma ya yi masu afuwa

-Yan ta’addan sun bayyana cewa sun gaji da ta’addanci da kuma azaba da yan kungiyar tsaro na sa kai ke basu

-Rundunar yan sanda ta jihar ta yi kira ga yan ta’addan da su mika wuya su tuba su daina ta’addanci saboda lokaci na kure masu

Wasu gungun yan ta’adda dake fakewa a dajin dake tsakanin karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina da karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna sun roki gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da a yi sulhu kuma ya yi masu afuwa.

Yan ta’addan sun bayyana wannan bukatar ta su ta bakin shugabansu, Malam Idris Yahaya, a wata tattaunawa ta musamman da ya shirya tsakaninshi da yan jarida a makarantar firamare ta Dankolo dake kusa da karamar hukumar Dandume. The Nation ta ruwaito.

Legit.ng ta binciko cewa Malam Idris Yahaya ya ce yan kungiyarshi sun gaji da ta’addanci da kuma azabtarwa da suke sha daga hannun yan kungiyar tsaron sa kai a kauyen.

Ya bayyana cewa sulhu da aka shiga kwanan nan tsakanin yan ta’addan da manoman kauyukan kan cewa kada yan ta’addan su hana manoma aikin gona shine ya assasa ganawarsa da yan jarida.

KARANTA WANNAN: Abin da yasa ake zargin mu da goyon bayan Boko Haram – Kungiyar agaji

Ya ce “Mun gaji da aikata ta'addanci, kuma mun gano cewa masu anfana da wannan ta’addanci manyan ma’aikatan gwamnati ne da jami’an tsaro, da suke so a cigaba saboda su cigaba da samun moriya.”

“Muna so gwamna Masari yayi magana da mu kai tsaye.” A cewarshi.

Yan ta’addan sun kuma bukaci gwamna Masari da ya taimaka wajen ganin an saki wasu shugabanninsu Lawal Baldu da Ibrahim Nakutama, da aka kama a filin jirgin sama shekaru biyu da suka wuce.

Yahaya ya bayyana cewa idan aka saki shugabannin na su, za su taimaka wajen kawo karshen ta’addanci da wuri.

Amma rundunar yan sanda ta jihar ta yi kira ga yan ta’addan da su tuba daga aikata ta’addanci su mika wuya saboda lokaci na kure masu.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ya bayyana cewa matakan tsaro kwarara da aka dauka sun taimaka kwarai wajen durkushe hare haren yan ta’adda a jihar Katsina.

Ya ce “Nan da yan satuttuka masu zuwa, babu sauran wajen boyo ga yan ta’adda. Ko su mika wuya ko kuma su dan dana kudarsu. Matakan tsaro da jami’an tsaro suka dauka hadi da taimakon al’umma na samar da sakamako mai kyau.” A cewarshi.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: