Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana abunda zai faru da kasar idan aka hana Almajiranci

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana abunda zai faru da kasar idan aka hana Almajiranci

Babban malamin addinin Musulunci kuma jagorar kungiyar darika na kasa, Sheikh Dahiru Bauchiyayi tsokaci akan shirin gwamnatin tarayya na dakatar da almajiranci a kasar.

Shehin Malamin ya kaulubalci gwamnati kan cewa har yaushe ne gwamnati za ta ciyar da masu bara su koshi alhalin tana fama da ma’aikatan ta.

Ya bayyana cewa ana kokarin hana miskinai hanyar neman abincinsu domin wasu ta hanyar barar ne suke samun abun kai wa bakin salati.

Dahiru Bauchi ya kuma ja kunnen gamnati kan cewa ta kiyaye domin kada ta janyo mumunan fitina a kasar.

Ya kara da cewa idan har aka matsa toh za su yi addu’a kan su miskinan nan Allah Ya maida su matsayin masu hana barar, su kuma masu hanawa Allah Ya maida su matsayin miskinan kuma Allah zai .

Yace “Wallahi aka hana bara ba a tanada musu abin da za su ci ba, masifar da za mu fada a kasar nan abin babu kyau. Su miskinan nan fa Allah Yana sonsu kamar yadda Yake son kowa, ba laifi suka yi wa Allah ba Ya maida su haka.

“A kiyaye, idan ba haka ba za mu jawo mummunar fitina a kasar nan. Idan kuma an matsa za mu yi addu’a su miskinan nan Allah Ya maida su matsayin masu hana barar, su kuma masu hanawa Allah Ya maida su matsayin miskinan kuma Allah zai amsa don haka a kiyaye.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Ganduje da Sanusi: Sheikh Dahiru Bauchi ya nemi karin mutane su shiga cikin lamarin

“Yanzu ma muna cikin bala’in yunwa da matsuwa da damuwa a kasa, mun rasa inda za mu sa kanmu saboda rikicin zagin waliyyai da kafirta Musulmi da ake yi ya jawo fushin Allah a kan kasa. Mutane suna karkashe mutane ba gaira ba dalili, sun hana mu zama lafiya saboda Allah Ya yi fushi ana gaba da waliyyanSa, ana zagin amajiransu ana kafirta Musulmi.

“Yanzu kuma ana so za a sake jawo mana wani babban bala’i na hana miskinai masu bara, ba a ba su abinci ba. Wannan abin da zai rikito da shi a Najeriya ya fi wanda muke ciki muni. Allah Ya shigar da wata mace wuta a Lahira saboda kyanwa, ta tare ta ba ta ba ta abinci ba, ba ta bar ta ta je ta nema da kanta ba har ta mutu, sai Allah Ya sa matar a wuta.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng