Allah ya kyauta: Uba ya yi ya ‘yar cikinsa cikin a Yobe

Allah ya kyauta: Uba ya yi ya ‘yar cikinsa cikin a Yobe

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Yobe ta kama wani mutumi mai suna Muhammadu Hassan bisa zarginsa da yiwa ‘yar cikinsa ciki.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe ne ya bayyana haka a yayin taron manema labarai a garin Damaturu.

Tun da farko dai jami'an ƴan sanda sun kama Muhammadu Hassan ne bayan zarginsa da saduwa da yar cikinsa mai kimanin shekaru 22 a duniya.

Wasu Rahotanni sun bayyana cewa budurwar na dauke da cikin mahaifinta na watanni biyar.

Wata majiya ta bayyana cewa Muhammadu Hassan ya sadu da yar ta sa ne har sau uku bayan da ya samu nasarar sanya mata kwayoyi a abin sha da kuma kosai.

KU KARANTA KUMA: Na tuna sanda nike zama cikin karuwai da yan jagaliya – Osinbajo

A wani lamari na daban, mun ji cewa rundunar yan sandan jihar Kaduna ta kama wani sojan Najeriya mai shekara 32, Lance Corporal Koza Yabiliok kan zargin siyar da alburusa ga masu garkuwa da mutane.

Rundunar ta kuma kama wasu masu laifi daban-daban har su 61 a fadin jihar cikin makonni biyu da suka gabata.

Lance Corporal Yabiliok wanda ke aiki a sansanin rundunar soji da ke Jaji, jihar Kaduna ya fada ma manema labarai yayinda aka gurfanar dashi cewa, yana siyar da kowani harsashi kan N400.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel