Atiku ya hallarci jana'izar surukinsa a Onitsha

Atiku ya hallarci jana'izar surukinsa a Onitsha

Dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar Peoples Democratic Party a zaben Fabrairun 2019, Atiku Abubakar a jiya Asabar ya hallarci jana'izar surukinsa, Cif Chukwuka Iwenjiora a garin Onitsha da ke jihar Anambra.

Tsohon shugaban kasa Goodlluck Jonathan da gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi suna dage cikin jerin manyan mutanen da suka hallarci jana'izar.

An haifi Iwenjiora, mahaifin matar Atiku, Jennifer ne a ranar 4 ga watan Yunin 1929 kuma ya rasu a ranar 26 ga watan Janairun 2019.

DUBA WANNAN: Kuma dai: An kara samun wata mata da ta caka wa mijinta wuka har ya mutu

A jawabin da ya yi wurin jana'izar, tsohon shugaban kasa Jonathan na bayyana marigayin a matsayin mutum mai hikima da tausayi.

Ya ce jajircewarsa wurin gina al'umma ne ya sanya shi farin jini a garinsu da ma kasa baki daya.

"Ya kasance mutum ne mai kaunar hadin kai da zaman lafiya kuma an yi babban rashi a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya," inji Jonathan.

A sakon ta'aziyarsa, Atiku ya bayyana surukinsa a matsayin "mutum mai kishin kasa da kuma kaunar kasarsa."

Atiku ya ce, "Babban abinda ya mayar da hankali a kai shine hadin kai da samarwa al'ummar mu tsaro tare da samar da ingantaccen ilimi da inganta zamantakewa tsakanin al'umma."

Ya ce marigayi Iwenjiora ya kan yi bakin jiki duk lokacin da wani abu da ka iya barazana ga hadin kan Najeriya ya faru.

A jawabinsa, Ihedioha ya ce marigayin dattijon mutum ne mai kishin kasa.

Iwenjiora ya rasu ya bar yara 13, jikoki 28 da tattaba kuni 9 da sauran 'yan uwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164