Jama'a ba su fita zaben kananan hukumomi ba a Jigawa
Mutane kadan ne suka fito kada kuri'unsu a zabukkan kananan hukumomi da aka gudanar a jihar Jigawa a yau Asabar 29 ga watan Yunin 2019.
Daily Trust ta ruwaito cewa tsirarun mutane kawai aka gano a layin zaben da wakilin ta ya ziyarci Duste da Kiyawa.
An gano mutane suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum a garin Dutse da Kiyawa.
Wani magidanci a Dutse da ya yi hira da majiyar Legit.ng, Sani Usman ya ce babu abokan hammay a zaben saboda babban jam'iyyar adawa a jihar wato Peoples Democratic Party (PDP) ba ta shiga zaben ba hakan ya sa bai tafi jefa kuri'a ba.
DUBA WANNAN: CBN za ta rage yawan kudaden da ke kewayawa a Najeriya, ta bayar da dalili
Wata mai sayar da abinci a Kiyawa wadda ta nemi a sakayya sunan ta ta ce ta bude shagon ta na sayar da abinci saboda ba ta da wata masaniya cewar ana gudanar da zabukkan kananan hukumomi a garin.
Jam'iyyar PDP ba ta shiga zaben ba saboda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Jihar Jigawa (JISIEC) ta hana ta takardun shiga takarar zabe.
Da ya ke tsokaci kan dalilin da ya sa PDP ba ta shiga zaben ba, Mataimakin Shugaban jam'iyyar na reshen Jigawa Ta Tsakiya, Aminu Jahun ya ce jam'iyyar tana duba yiwuwar zuwa kotu ne domin kallubalantar matakin da JISIEC ta dauka.
Da aka tuntunbe shi kan batun, Mai magana da yawun JISIEC, Habu Babura ya ce jam'iyyar PDP ta zo sayan fom din ne bayan wa'addin da aka bayar na sayarwa ya kare.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng