Daga karshe, APC ta zabi shugabannin majalisa 4, Sanata Abdullahi Adamu ne shugaban masu rinjaye
- Sanata Abdullahi Adamu, Ajayi Borrofice sun shugabannin masu rinjaye a majalisar dattawa
- Sanata Orji Uzor Kalu, Yahya Abdullahi sun zama bulalan majalisar dattawa
- Ana sauraron na majalisar wakilai nan zuwa ranar Talata
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta zabi tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, hakazalika tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, matsayin bulaliyar majalisa.
Sanata Ajayi Borrofice ne mataimakin shugaban masu rinjaye, yayinda Sanata Yahya Abdullahi ya zama mataimain bulaliyar majalisar dattawa. Wannan ya bayyana ne bayan ganawar shugabannin APC a birnin tarayya Abuja.
Da farko, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ake kyautata zaton zai samu kujeran shugaban masu rinjaye kasancewarsa na hannun daman shugaban majalisar, Ahmad Lawan. Amma daga karshe, bai samu ba.
KU KARANTA: Saraki ya sace N12bn daga asusun jihar Kwara - EFCC
Ana sa ran za'a alanta wannan labari ranar Talata idan majalisar dattawa ta dawo daga hutu.
Bayan haka, ana sauraron sunayen shugabannin majalisar wakilai kafin ranar Talata. Har yanzu ba'a san wadanda zasu samu shiga ba.
Makonni biyu da suka gabata, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta alanta sunayen shugabanninta a majalisun guda inda Sanata Eyinnnaya Abaribe ya zama shugaban marasa rinjaye.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng