Dandalin Kannywood: Na fiso na fito a matsayin fitsararriya a film - Maryam Yahaya

Dandalin Kannywood: Na fiso na fito a matsayin fitsararriya a film - Maryam Yahaya

- Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya ta bayyana bangaren da ta fi so a dinga sanyata a fim

- Jarumar ta ce tafi so a dinga sanyata a matsayin fitsararriya a fim

- Amma ta ce a gaske ita ba fitsararriya bace, kawai tana son fitowa a wannan fannin ne saboda taga masoyanta suna son ganin tana taka rawa a fannin

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa na Kannywood, Maryam Yahaya ta bayyana wani sirri da tafi so a masana'antar, inda ta ce tafi so taga an bata bangaren da zata fito a matsayin fitsararriya a film.

Maryam Yahaya ta bayyana hakanne a lokacin da take tattaunawa da wakilan tashar Freedom Radio na jihar Kano, a cikin shirin Taurarunmu da suke gabatarwa ranar Alhamis.

Sai dai kuma jarumar ta bayyana cewa a zahiri ita ba fitsararriya bace, ta ce tana son wannan fannin ne, saboda yadda ta fahimci cewa masoyanta suna son ganin tana taka rawa a irin wannan bangaren.

KU KARANTA: Jin dadi na inda yake: An ba wa wata jaririya kyautar tikitin jirgi na tsawon shekara 25, saboda an haifeta a cikin jirgi

A hirar da aka yi da jarumar a cikin shirin, Maryam ta tattauna batutuwa da yawan gaske, musamman irin rawar da ta taka a cikin shirin fim din SARINA.

A karshe jarumar ta yiwa masoyanta addu'ar fatan alkhairi, inda ta bayyana musuc cewar suna nan a ranta a koda yaushe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng