Ku karbe ragamar shugabanci a kasar – Obasanjo ga matasa

Ku karbe ragamar shugabanci a kasar – Obasanjo ga matasa

- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bukaci matasa da su nemi takarar mukaman shugabanci a kasar

- Obasanjo ya bukaci matasan da kada su bari kowa ya yaudare su da cewar sun yi kankanta wajen neman shugabanci

- Jigon kasar ya nuna damuwa kan yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo jiya Alhamis, 27 ga watan Yuni, ya bukaci matasa da su nemi takarar mukaman shugabanci a kasar.

Yayin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar matasan Najeriya a gidansa da ke harabar dakin karatunsa a Abeokuta, Obasanjo ya ce: “kada ku bari kowa ya fada muku cewa kun yi kankanta da neman shugabanci, na soma bada gudumuwana a duniya a lokacin da nake aiki a kasar Congo a shekarar 1960, a lokacin ina dan shekaru 24.

"A lokacin da na tafi filin daga na kasance dan kasa da shekara 35, a lokacin ne na zama shugaban kasa a mulkin soja, ban kai shekaru 40 ba a lokacin."

KU KARANTA KUMA: Majalisar Buhari: Za a bayyana sunayen ministoci a watan Yuli – Sakataren tarayya

Obasanjo ya nuna damuwa cewa sama da yara miliyan 13 ne basa zuwa makaranta a Najeriya.

Yace: “duk abin da nayi, nayi ne saboda na kasance mai ilimi kuma mai kishin kasar Najeriya.

“Da banyi karatu ba da ban kai matsayin yin abubuwan da nayi ba, a yau ina matukar bakin cikin cewa fiye da yaran Najeriya miliyan 13 wadanda ya kamata suna a makaranta sun bar makaranta.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng